Ana Shirin Ballowa Tsohon Gwamna Ruwa, Ya Yi Barazana ga Masu Son Hada Shi da Tinubu

Ana Shirin Ballowa Tsohon Gwamna Ruwa, Ya Yi Barazana ga Masu Son Hada Shi da Tinubu

  • Tsohon gwamnan Kogi da ke fuskantar shari'a bisa zargin almundahana ya musanta fadin munanan kalamai a kan shugaban kasa
  • Ta cikin wata sanarwa da daraktan yada labaran tsohon gwamnan, Ohiare Michael, ya fitar, Yahaya Bello ya fusata da zancen da ake yi
  • Ya zargi 'yan siyasa marasa kishin kasa da son bata kyakkyawar alakar da ke tsakaninsa da shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

FCT Abuja - Tsohon gwamnan Kogi, Yahaya Bello ya fusata bayan an fara yada labarin da ke son hada shi rigima da shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu.

Tsohon gwamnan Kogi, Yahaya Bello, ya karyata labarin da wata kafar yada labarai ta fitar da ke cewa ya na caccakar Mai girma Bola Tinubu.

Kara karanta wannan

A karshe, Jonathan ya samu damar gwabzawa da Tinubu a 2027

Yahaya
Tsohon gwamnan Kogi zai shigar da jarida kara a gaban kotu Hoto: Alhaji Yahaya Bello
Asali: Facebook

Jaridar Punch ta wallafa cewa daraktan yada labaran tsohon gwamnan, Ohiare Michael, ya ce babu hadin wadancan kalaman batanci da Yahaya Bello.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Tsohon gwamna, Yahaya Bello zai nufi kotu

Jaridar PM News ta ruwaito cewa tsohon gwamnan Kogi, Yahaya Bello ya yi barazanar maka kafar da ta fitar da labarin cewa ya soki Tinubu.

Sanarwar da Ohiare Michael ya fitar ta ce;

“Da farko, ba mu maida hankali kan irin wannan labari mara tushe, domin babu wani dan Najeriya mai ilimi da zai dauki irin wannan batu mai ban dariya da muhimmanci, musamman ma tun da rubutun kotu abubuwa ne a fili.

Dalilin martanin Yahaya Bello kan sukar Tinubu

Daraktan yada labaran tsohon gwamnan, Ohiare Michael ya bayyana dalilin da ya sanya su mayar da martani kan labarin da ke alakanta Yahaya Bello da sukar Bola Tinubu.

Ya bayyana rahoton a matsayin wani bangare na makirci daga wasu ‘yan siyasa marasa kishin kasa da ke kokarin bata dangantaka mai kyau tsakanin shugaba Tinubu da tsohon gwamna.

Kara karanta wannan

'Saurin me ake yi?" Dattawan Arewa sun shawarci gwamnati kan kudirin harajin Tinubu

Wata jaridar kafar yanar gizo ta jingina Yahaya Bello da kalaman da ke cewa zai tona asirin yadda Tinubu ya zama shugaban kasa, da wasu kalaman da aka ce ya fada.

Kotu ta ba da belin Yahaya Bello

A baya, mun ruwaito cewa babbar kotun tarayya da ke zamanta a Abuja ta bayar da belin tsohon gwamnan Kogi, Yahaya Bello bayan EFCC ta sake gurfanar da shi a gabanta.

Kotun ta bayar da belinsa a kan N500m, tare da bukatar ya mika fasfonsa na kasa da kasa tare da dakatar da tafiye-tafiye zuwa waje ba tare da izini ba da sauran sharudda.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.