Gwamna Ya Bi Sahun Tinubu, Ya Kafa Irin Ma'aikatar da Ya Kirkiro a Jihar Yobe

Gwamna Ya Bi Sahun Tinubu, Ya Kafa Irin Ma'aikatar da Ya Kirkiro a Jihar Yobe

  • Gwamnan jihar Yobe, Mai Mala Buni ya kwaikwayi shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu wajen samar da sabuwar ma'aikatar kula da kiwon dabbobi
  • Mai Mala Buni ya amince a kafa ma'aikatar inda ya umarci sakataren gwamnatin jihar da kwamishinan noma su tsara ayyukan da za ta gudanar
  • A cikin shekara shida da ya yi yana mulki a jihar Yobe, Gwamna Buni ya kafa sabbabin ma'aikatu guda uku da hukumomin gwamnati guda 13

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Yobe - Gwamnan jihar Yobe, Mai Mala Buni, ya amince da kafa ƙarin sabuwar ma’aikata.

Gwamna Mai Mala Buni ya amince da kafa sabuwar ma'aikatar kula da kiwon dabbobi nan take.

Gwamnan Yobe ya kafa sabuwar ma'aikata
Gwamna Mai Mala Buni ya kafa ma'aikatar kula da kiwon dabbobi Hoto: Hon. Mai Mala Buni
Asali: Facebook

Gwamnan Yobe ya kafa sabuwar ma'aikata

Amincewar kafa sabuwar ma’aikatar na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da sakataren yaɗa labaran sakataren gwamnatin jihar (SSG), Alhaji Shuaibu Abdullahi ya fitar, cewar rahoton jaridar Leadership.

Kara karanta wannan

Kirismeti: Gwamna Zulum ya yi wa ma'aikata gata a Borno

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Gwamna Buni ya umarci SSG, shugaban ma’aikatan gwamnati da kwamishinan ma’aikatar gona da su tsara ayyukan sabuwar ma’aikatar.

Gwamnna ya kuma umarci su samar mata da ofis, tura ma’aikata domin tabbatar da fara aikin ma’aikatar cikin gaggawa, rahoton jaridar Daily Trust ya tabbatar.

Gwamna Buni ya samar da ma'aikatu a Yobe

Kafa sabuwar ma’aikatar kula da kiwon dabbobin, ta sanya Gwamna Buni ya samar da cikakkun ma’aikatu guda uku a cikin shekaru shida na gwamnatinsa a jihar.

Sauran ma’aikatun biyu sun haɗa da ma’aikatar jin ƙai da walwala da kuma ma’aikatar samar da ayyukan yi.

Hakazalika, a cikin shekara shidan da suka gabata, gwamnan ya yi nasarar samar da hukumomi 13 da ke da niyyar inganta rayuwar al’umma a faɗin jihar.

A matsayinta na ɗaya daga cikin jihohin da ke kan gaba wajen kiwo, samar da sabuwar ma’aikatar kula da kiwon dabbobin na ƙara jaddada ƙudirin Gwamna Buni na bunƙasa tattalin arziƙin jihar domin samun ci gaba.

Kara karanta wannan

Kirisimeti: Gwamna ya gwangwaje ma'aikata da kudin hutu, zai raba masu N150,000

Gwamna Buni ya yi rabon tallafi a Yobe

A wani labarin kuma, kun ji cewa gwamnan jihar Yobe, Mai Mala Buni, ya yi rabon tallafi ga mutanen da suka samu asara sakamakon ambaliyar ruwa.

Gwamna Mai Mala Buni ya ba da tsabar kuɗi N2bn ga mutane 25,000 da suka haɗa da waɗanda ambaliyar ruwan ta shafa da kuma marasa galihu.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng