Kotu Ta Zauna kan Shari'ar 'Yan Boko Haram, Miyagu 325 Sun San Makomarsu
- Kotu ta sake zama a karo na biyar da shida domin yanke wa ƴan Boko Haram hukunci a kan zargin laifuffuka da dama
- A waɗannan lokuta, an yanke hukunci bayan sauraron shari'ar mutane 325 da ake zargi da miyagun ayyuka
- Wannan na kunshe a sanarwar da cibiyar yaki da ta’addanci ta kasa, ofishin NSA ya fitar a yammacin ranar Lahadi
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Niger - Ɗaruruwan ƴan ƙungiyar tayar da ƙayar baya ta Boko Haram ne su ka san makomarsu bayan sun kashe dubban mutane a Arewa maso Gabas.
Kotun da ta zauna a wurin adana masu laifi na Kainji da ke Niger, ta yanke hukunci a kan ƴan Boko Haram guda 325 a zaman na na biyar da shida.
Jaridar Punch ta wallafa cewa miyagun ƴan Boko Haram da jami'an tsaron kasar nan su ka kama da dama ne ake gurfanar da su a gaban kotun sannu a hankali don tsintar ribar mugun aikinsu.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Kotu ta ɗaure ƴan Boko Haram
Daily Post ta ruwaito cewa kotu da ke zamanta. Niger ta yanke wa wasu daga cikin ƴan ƙungiyar Boko Haram ɗaurin shekaru 70 kowanensu.
A zaman kotun na biyar a watan Yuli a jerin ci gaba da sauraron shari'ar mugayen, an saurari shari'ar mutane 143, an yi nasarar daure 125
A zama na shida, an saurari shari'ar mutane 237 kuma an kama akalla mutane 200 da laifuffukan ta'addanci.
An yanke wa yan Boko Haram hukunci
Sanarwar da cibiyar yaki da ta’addanci ta kasa, ofishin mai bai wa shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro ta fitar a ranar Lahadi, ta ce an yanke wa ƴan Boko Haram hukuncin kisa.
Sanarwar ta ƙara da cewa an yanke wa ‘yan ta’adda hukuncin kisa zuwa daurin rai da rai da kuma shekaru 20 zuwa 70
Hukuncin ya danganta da girman laifukan da suka aikata.
Kwamandan Boko Haram ya miƙa wuya
A wani labarin, kun ji cewa wani babban kwamandan kungiyar Boko Haram, Bochu Abacha ya zubar da makamansu, tare da miƙa wuya ga dakarun sojojin ƙasar nan.
A sanarwar da rundunar MNJTF ta fitar, ta tabbatar da cewa Abacha ya fara ba su haɗin kai ta hanyar miƙa masu bayanan sirri domin ƙara yaƙar ta'addanci a Arewa maso Gabas.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng