"Ka Watsar da Su": Gwamnan PDP Ya ba Shugaba Tinubu shawara

"Ka Watsar da Su": Gwamnan PDP Ya ba Shugaba Tinubu shawara

  • Gwamnan jihar Bauchi ya ci gaba da bayar da shawarwari ga shugaban ƙasan Najeriya, mai girma Bola Ahmed Tinubu
  • Sanata Bala Mohammed na jam'iyyar PDP ya buƙaci shugaban ƙasan da ya kori tarkacen da ke cikin gwamnatinsa
  • Gwamnan ya nuna cewa wasu daga cikin ƴan majalisar zartaswa na gwamnatin Bola Tinubu suna ɓata ƙoƙarin da yake yi

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Rivers - Gwamnan jihar Bauchi kuma shugaban ƙungiyar gwamnonin PDP, Bala Mohammed, ya ba shugaban ƙasa Bola Tinubu, shawara.

Gwamna Bala Mohammed ya buƙaci Shugaba Tinubu da ya cire abin da ya bayyana a matsayin tarkace a cikin gwamnatinsa.

Gwamna Bala ya ba Tinubu shawara
Gwamna Bala Mohammed ya ba Bola Tinubu shawara Hoto: Senator Bala Abdulkadir Mohammed, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu
Asali: Facebook

Wace shawara aka ba Bola Tinubu

Gwamna Bala Mohammed ya bayyana hakan ne a matsayin babban baƙo na musamman, wajen ƙaddamar da titin Umuakali-Eberi mai tsawon kilomita 14.1 a ƙaramar hukumar Omuma ta jihar Rivers, cewar rahoton tashar Channels tv.

Kara karanta wannan

Ministan shari'a ya fadi shugabannin kananan hukumomin da za a garkame

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A cewar Gwamna Bala Mohammed, yayin da gwamnonin ke da ƙwarin gwiwa a kan shugabancin Tinubu, ayyukan wasu ƴan majalisar zartaswarsa na kawo cikas ga ƙoƙarin da yake yi.

Ya ce dole ne Shugaba Tinubu ya watsar da tarin tarkacen da suka yi masa yawa a gwamnatinsa, yana mai jaddada buƙatar daukar ƙwararan matakan da suka dace.

Gwamna Bala ya yabi Fubara

Gwamna Bala ya yabawa gwamnan jihar Rivers, Siminalayi Fubara bisa yadda yake gudanar da shugabanci nagari duk da ƙalubalen siyasar da ya ke fuskanta.

Gwamnan ya bayyana ƙwarin gwiwar cewa gwamnan na yin shugabanci yadda ya kamata.

Ya ce bisa ga abin da ya gani, ya daina damuwa kan ƙoƙarin Gwamna Fubara ko kuma yadda jama’a suke kallonsa game da gwamnatinsa.

Sakataren gwamnatin Bauchi ya yi murabus

A wani labarin kuma, kun ji cewa gwamnatin jihar Bauchi ta samu giɓi bayan sakataren gwamnati (SSG) ya yi murabus daga muƙaminsa.

Ibrahim Kashim ya yi murabus daga mukaminsa nan take, amma bai bayyana dalilinsa na yin hakan ba, sai dai ana hasashen da yiwuwar ya tsaya takarar gwamna a zaɓen shekarar 2027.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng