Kaduna: Gwamna Uba Sani Ya ba da Sabon Mukami a Gwamnatinsa

Kaduna: Gwamna Uba Sani Ya ba da Sabon Mukami a Gwamnatinsa

  • Gwamnan jihar Kaduna, Sanata Uba Sani ya naɗa mai ba shi shawara na musamman kan harkokin ƙananan hukumomi
  • Uba Sani ya ɗauko tsohon shugaban ƙaramar hukumar Kaduna ta Kudu, Ƙabiru Yakubu Jarimi, a matsayin wanda zai riƙe kujerar
  • Naɗin da Gwamna Uba Sani ya yi wa tsohon shugaban ƙaramar hukumar zai fara aiki ne nan take

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Kaduna - Gwamnan jihar Kaduna, Sanata Uba Sani, ya ba tsohon shugaban ƙaramar hukumar Kaduna ta Kudu, Kabiru Yakubu Jarimi, muƙami a gwamnatinsa.

Gwamna Uba Sani ya naɗa Kabiru Yakubu Jarimi a matsayin mai ba shi shawara na musamman kan harkokin ƙananan hukumomi.

Uba Sani ya ba da mukami a gwamnatinsa
Gwamna Uba Sani ya ba Kabiru Yakubu Jarimi mukami a gwamnatinsa Hoto: @ubasanius
Asali: Twitter

Hakan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da babban sakataren yaɗa labaran gwamnan, Ibraheem Musa ya fitar, kuma ya rabawa manema labarai a Kaduna ranar Asabar, cewar rahoton jaridar Tribune.

Kara karanta wannan

"Ka watsar da su": Gwamnan PDP ya ba Shugaba Tinubu shawara

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Uba Sani ya naɗa muƙami

Naɗin da Gwamna Uba Sani ya yi wa Kabiru Yakubu Jarimi zai fara aiki ne nan take.

The Cable ta rahoto cewa sanarwar ta ce ana sa ran Kabiru Jarimi zai yi amfani da gogewar da yake da ita a harkokin mulki na ƙananan hukumomi, domin ya yi fice a sabon muƙamin da aka ba shi.

"Gwamna ya buƙaci Kabiru Jarimi da ya sauke nauyin da ya rataya a wuyansa cikin jajircewa, sadaukarwa da adalci, tare da yi masa fatan Allah ya ɗora shi a kan daidai ya kuma ba shi kariya."

- Ibraheem Musa

Wanene Kabiru Yakubu Jarimi?

Kabiru Yakubu Jarimi ƙwararren jami'in gwamnati ne wanda ya samu gogewa a harkokin mulki.

Ya yi wa’adi biyu a matsayin zaɓaɓɓen shugaban ƙaramar hukumar Kaduna ta Kudu, kuma ya yi fice a kan manufofinsa na kawo ci gaba ga al’umma, da samar da ci gaba mai ɗorewa.

Kara karanta wannan

Shugaban majalisa ya fadi ainihin dalilin Tinubu na ba Wike mukamin minista

Gwamna Uba Sani ya yi garambawul

A wani labarin kuma, kun ji cewa gwamnan jihar Kaduna, ya yi garambawul a majalisar zartawa ta jihar yayin da ya kori wani kwamishina.

Gwamna Uba Sani ya kori kwamishinan tsaron cikin gida da harkokin cikin gida, Samuel Aruwan daga kan muƙaminsa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng