Kirismeti: Gwamna Zulum Ya Yi Wa Ma'aikata Gata a Borno

Kirismeti: Gwamna Zulum Ya Yi Wa Ma'aikata Gata a Borno

  • Ma'aikata a jihar Borno za su samu albashinsu na watan Disamban 2024 da wuri domin tunkarar bukukuwan ƙarshen shekara
  • Gwamna Babagana Umara Zulum ya amince a biya ma'aikata da ƴan fansho albashin watan Disamban a ranar Juma'a, 13 ga wata
  • Zulum ya amince da biyan kuɗaɗen domin ba Kiristoci da sauran mabiya addinai damar shiryawa bukukuwan da ke tafe

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Borno - Gwamnan jihar Borno, Farfesa Babagana Umara Zulum, ya amince a biya ma'aikata albashi.

Gwamna Zulum ya amince da biyan albashin watan Disamba ga dukkan ma'aikatan gwamnati da ke karɓar kuɗi daga gwamnatin jihar.

Zulum ya umarci a biya albashi
Zulum ya amince a biya ma'aikata albashin watan Disamban 2024 Hoto: @ProfZulum
Asali: Facebook

Hakan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Dauda Iliya ya fitar a ranar Asabar, cewar rahoton jaridar The Punch.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Zulum ya amince a ba ma'aikata albashi

Kara karanta wannan

Kirisimeti: Gwamna ya gwangwaje ma'aikata da kudin hutu, zai raba masu N150,000

Sanarwar ta ce Gwamna Zulum ya amince da biyan kuɗin ne a ranar Juma’a, 13 ga watan Disamba, 2024.

Sanarwar ta nuna cewa dalilin biyan kuɗaɗen shi ne domin a taimaki Kiristoci da sauran mabiya addinai su shirya bukukuwan ƙarshen shekara a kan lokaci.

"Umarnin da gwamnan ya bayar domin biyan kuɗi da wuri a Disamba, ya yi daidai da jajircewarsa wajen tafiya da kowa, da ba jama'a damar shiryawa bukukun ƙarshen shekara ba tare da matsalar rashin kuɗi ba."
"Farfesa Babagana Zulum ya sake kyautatawa, yayin da albashi da fansho na watan Disamban 2024 ya fara sauka a asusun ma'aikata, domin tabbatar da Kiristoci da sauran mabiya addinai sun shiryawa bukukuwan da ke tafe a kan lokaci."

- Dauda Iliya

Sanarwar ta ƙara da cewa Gwamna Zulum ya yi kira ga ma'aikatan da su ci gaba da yin addu’o’in samun zaman lafiya a jihar Borno da ma kasa baki ɗaya.

Kara karanta wannan

Nasarawa: Ma'aikata za su fara walwala da gwamna ya yi alkawarin biyan N70,500

Gwamna Zulum ya maida yara makaranta

A wani labarin kuma, kun ji cewa gwamnan jihar Borno, Farfesa Babagana Umara Zulum ya bayyana cewa ya rage adadin yawan yaran da ba sa zuwa makaranta.

Gwamna Zulum ya ce ya zuba jari sosai a fannin ilimi a cikin shekara biyar da suka gabata, da suka haɗa da gina makarantu 104 da gyara ajujuwa 2,931.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng