Magana Ta Kare, CBN Ya Yi Magana kan Daina Amfani da Tsofaffin Kuɗi a Karshen 2024

Magana Ta Kare, CBN Ya Yi Magana kan Daina Amfani da Tsofaffin Kuɗi a Karshen 2024

  • Babban banki CBN ya bukaci ƴan Najeriya su yi fatali da jita-jitar da ake yaɗawa cewa za a daina amfani da tsofaffin kudi a karshen 2024
  • CBN ya nanata cewa babu ranar daina amfani da kowane irin takardun kudi, tsoho ko sabo duba da hukuncin da kotun koli ta yanke
  • Bankin ya jaddada cewa za a ci gaba da hada-hada da tsofaffin N1,000, N500 da N200 har illa masha Allahu ba tare da wani wa'adi ba

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Abuja - Babban bankin Najeriya watau CBN ya sake nanata cewa tsofaffin takardun N200, N500, da N1,000 za su ci gaba da amfani har illa masha Allahu.

CBN ya ce hukuncin da kotun ƙoli ta yanke ranar 29 ga watan Nuwamba, 2024 ya halatta amfani da tsofaffin kudin har sai ranar da aka wayi gari babu su.

Kara karanta wannan

Belin N500m: Kotu ta saki belin Yahaya Bello, an kafa masa sharuda masu tsauri

Cardoso da Naira.
Bankin CBN ya jaddada halascin amfani da tsofaffin takardun kudi Hoto: @Cenbank
Asali: Getty Images

Za a haramta amfani da tsofaffin Naira?

Hakan na kunshe ne a wata sanarwa da CBN ya wallafa a shafin X nai ɗauke da sa hannin daraktan sadarwa na babban bankin Sidi Ali Hakama.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Bankin ya ce domin share shakku babu ranar haramta amfani da dukkan nau'in kuɗin Najeriya tsofaffi da sababbin N1,000, N500, N200 da tsohuwar N100.

CBN ya ce ya sake jaddada halaccin amfani da takardun kudin ne sakamakon wata jita-jita da ta fara cin kasuwa cewa tsofaffin kudin na dab ba zama haramun.

Bankin CBN ya share duk wata tantama

"Kamar yadda CBN ya yi bayani a baya, bankin na kara tabbatarwa yan Najeriya cewa hukuncin kotun koli na watan Nuwamba ya halatta amfani da tsofaffin N1,000, N500 da N200 har illa ma sha Allah.
"Don haka, muna ba jama’a shawara da su yi watsi da duk wani iƙirari na cewa tsohon takardun kuɗin da aka ambata za su daina amfani a ranar 31 ga Disamba, 2024.

Kara karanta wannan

Rikici ya kunno kai a tsakanin gwamnonin jihohi 36 kan kudirin harajin Tinubu

- Sidi Ali Hakama.

CBN ya bukaci ƴan Najeriya su ci gaba da harkokinsu na yau da kullum da takardun kudi, tsofaffi da sababbi ba tare da wata fargaba ba.

A wani labarin, kun ji cewa Majalisar Wakilai ta nuna damuwa kan karancin takardun kudin da ake fama da shi a bankunan kasuwanci da ke faɗin kasar nan.

Hakan ya sa Majalisar ta yi kira ga babban bankin kasa watau CBN ya gaggauta magance wannan matsala da ta kara jefa ƴan Najeriya cikin wahala.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262