Kwana Ya Ƙare: Mata da Miji Sun Rasu Ta Hanya Mai Ban Tausayi a Jihar Kano
- Allah ya yi wa mata da miji rasuwa sakamakon ibtila'in gobara da ya afku a Rangaza, ƙaramar hukumar Ungogo a Kano
- Hukumar kashe gobara ta Kano ta tabbatar da mutuwar ma'auratan, ta ce sun mutu ne sakamakon raunuka da hayaƙin da suka shaƙa
- Jami'in hulɗa da jama'a na hukumar, Saminu Yusif Abdullahi ya ce yanzu haka an fara bincike don gano maƙasudin tashin gobarar
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Kano - Wani magidanci ɗan shekaru 67, Muhammad Uba da matarsa Fatima Muhammad mai shekaru 52 sun mutu a wata gobara da ta tashi a Kano.
Lamarin ya faru ne a ranar Juma’a a unguwar Rangaza (Inken) Layin AU da ke karamar hukumar Ungogo a jihar Kanon dabo.
Jami'in hulɗa da jama'a na hukumar kashe gobara ta jihar Kano, Saminu Yusif Abdullahi ya tabbatar da faruwar lamarin, kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Yadda mata da miji suka mutu a Kano
Saminu Yusif Abdullahi ya ce hukumar ta samu kiran neman ɗaukin gaggawa da misalin karfe 01:45 da tsakar dare wayewar garin yau Juma'a da wani jami'inta, FS Ahmad Abubakar.
"Jami'an da ke bakin aiki a ofishinmu da ke Bompai sun garzaya wurin da lamarin ya faru inda suka isa da misalin karfe 01:51 na safe."
"Lokacin da suka isa sun tarar da an samu nasarar shawo kan wutar, ɗakuna biyu sun ƙone. Wani magidanci, Muhammad Uba (67) da matarsa Fatima Muhammad (52) sun shaki hayaƙi da yawa "
"Ma'auratan sun fita hayyacinsu a lokacin da aka ciro su daga cikin gidan kuma sun ji raunuka, daga baya likitoci suka tabbatar da rai ya yi halinsa."
Hukumar kwana-kwana ta fara bincike
Saminu ya kara da cewa daga bisani sun mika gawarwakin mata da mijin ga mai unguwa Muhammad Auwalu Rayyanu na Rangaza a karamar hukumar Ungogo.
Ya ce a halin yanzu jami'an hukumar kwana-kwana sun fara bincike domin gano musabbabin tashin gobarar, cewar Leadership.
Gobara ta tafka ɓarna a Legas
A wani labarin, kun ji cewa ƴan kasuwa sun shiga jimami a jihar Legas bayan tashin wata mummunar gobara a fitacciyar kasuwar Alaba Rago
Gobarar da ta tashi cikin tsakar dare a kasuwar da ke a unguwar Ojo ta yi sanadiyyar lalata kayayyaki na miliyoyin Naira.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng