Darajar Naira Ta Samu Koma baya, Ta Rikito a Kasuwar Musayar Kudi a Najeriya
- A karo na biyu a jere, Dalar Amurka ta kara tashi a kasuwar canji ta bayan fage ranar Alhamis, 12 ga watan Disambar 2024
- Bayanai sun nuna cewa darajar Naira ta sauka zuwa N1,668 daga farashin da aka yi cinikin kowace Dala kan N1,600 a ranar Laraba
- Sai dai kuma a ɗaya ɓangaren darajar kudin Najeriya ta farfaɗo a kasuwar gwamnati, inda Dala ta rikito zuwa N1,534.6
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Abuja - Darajar kuɗin Najeriya watau Naira ta kara faɗuwa a kasuwar hada-hadar musayar kudi ta bayan fage wacce aka fi sani da kasuwar ƴan canji.
A jiya Alhamis, 12 ga watan Disamba, 2024, Naira ta sake rikitowa zuwa N1,668 kan kowace Dalar Amurka daga farashin N1,600/1$ da aka yi ciniki ranar Laraba.
Tribune Nigeria ta ce wannan faɗuwa na nuna babban koma baya ga darajar kudin a kasuwar bayan fage ma'ana ba ta hukuma ba.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Naira ta kara daraja a kasuwar gwamnati
Sabanin haka kuma Naira ta kara karfi a kasuwar canji ta gwamnati, inda Dalar Amurka ta rikito ƙasa zuwa N1,534.6.
Hakan dai na cikin rahoton kasuwar musayar kudi ta gwamnati watau NFEM wanda babban bankin Najeriya (CBN) ya wallafa ranar Alhamis.
Ƙimar Naira a farashin gwamnati ya ƙaru da N10.4 idan aka kwatanta da farashin da aka yi ciniki a ranar Laraba da ta shige.
Banbancin farashin ƴan canji da gwamnati
Wannan ya sa banbancin farashin da ake samu tsakanin kasuwar hukuma da ta ƴan canji ya ƙaru zuwa N133.4 daga N55 a makon jiya.
Karo na biyu kenan a jere Naira na faɗuwa kan Dalar Amurka a kasuwar bayan fage a cewar rahoton Vanguard.
An ruwaito cewa ƙimar Naira ta ragu a ranar Laraba, inda ta faɗo zuwa N1,600 daga N1,585 da aka sayi kowace Dala a ranar Talata.
Dalilin da ba son farfaɗowar Naira
A wani labarin, kun ji cewa rsohon hadimin shugaban kasa, Reno Omokri ya soki ƴan kasar nan da ba su fata mai kyau ga ci gaban darajar Naira a kasuwar canji.
Ya bayyana haka ne a lokacin da darajar Naira ta jera kwanaki biyu ta na samun kanta a kasuwar musayar kuɗaɗe.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng