Sanata Ta Fusata, Ta Fice daga Zauren Majalisa a kan Hana Wike Rusau a Abuja
- Sanata mai wakiltar Babban birnin tarayya, Ireti Kingibe ta fusata da yadda Godswill Akpabio ya so tura shirinta gaba
- Tun da fari, an tsara 'yar majalisar za ta gabatar da wani kudiri a ranar Laraba, sai aka dage zuwa Alhamis, nan ma aka so dagewa
- Wannan ya sa ta fice daga majalisar, amma daga baya sai shugaba Godwill Akpabio ya nemi ta dawo tare da gabatar da kudirin
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
FCT Abuja - An samu hayaniya a Majalisar Dattawa ranar Alhamis yayin da Sanata Ireti Kingibe mai wakiltar Babban Birnin Tarayya ta fice daga zaman majalisar.
‘Yar majalisar ta dauki matakin ne domin nuna fushi a kan yadda shugaban majalisa, Godswill Apkabio ya dakile ta daga gabatar da kudirinta.
Jaridar Daily Trust ta wallafa cewa Sanata Ireti Kingibe ta nuna rashin jin dadi tun da fari a kan yadda Ministan Abuja, Nyesom Wike ke rusau ba-ji-ba-gani.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Sanata ta fusata a majalisar dattawa
Legit.ng ta ruwaito cewa Sanata Kingibe ta yi niyyar gabatar da kudirinta a ranar Larabar da ta gabata, amma aka dage zuwa ranar Alhamis, amma duk da haka aka nemi dage hakan.
Wannan ya sa ta fusata, tare da ficewa daga cikin majalisar a cikin fushi, lamarin da ya sa daga bisani, Sanata Godswill Akpabio ya bukaci a nemo ta.
An nemi Sanata ta ba majalisa hakuri
Shugaban majalisar dattawa, Sanata Godswill Akpabio ya umarci ‘yar majalisa mai wakiltar Abuja da ta bayar da hakuri ga takwarorinta bayan ta fice daga cikin zauren majalisar.
Wannan na zuwa bayan ya aika an kira Sanata Kingibe ta gabatar da kudirinta, kamar yadda aka tsara tun da da fari, lamarin da majalisa ta amince da hana Nyesom Wike rusau a Abuja.
Majalisa za ta binciki gwamnatin Buhari
A wani labarin, mun ruwaito cewa majalisar wakilan kasar nan za ta fara binciken wasu kudi da gwamnatin Muhammadu Buhari ta karbo rance daga Bankin Duniya.
Matakin ya biyo bayan kudirin dan majalisa, Chike Okafor ya gabatar, ya na tuhumar yadda ake samun karuwar matsalolin abinci mai gina jiki a tsakanin 'yan Najeriya.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng