Batutuwa 30 Sun Jawo Taron ECOWAS a Najeriya, Ministoci Sun Hallara a Abuja
- Ministocin ƙungiyar ci gaban tattalin kasashen Afrika ta Yamma (ECOWAS) sun fara gudanar da taro a Abuja
- Za a duba manyan batutuwa da su ka shafi yankin nahiyar da matsalolin da ƙasashen ke fuskanta a halin yanzu
- A yayin jawabin buɗe taro, an fara faɗar guda daga cikin ƙalubalen da kungiyar ECOWAS kanta ke fuskanta
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
FCT Abuja - Majalisar Ministocin Kungiyar Tattalin Arzikin Kasashen Yammacin Afirka (ECOWAS) ta gudanar da zaman ta na 93 a hedikwatar ECOWAS da ke Abuja. Zaman, wanda Ministan Harkokin Wajen Najeriya, Ambasada Yusuf Tuggar, ya jagoranta, zai mayar da hankali kan batutuwan muhimmanci ga shiyyar.
Channels Television ta wallafa cewa wasu daga cikin abubuwan da za duba sun hada da na manufofin tattalin arziki, da kuma hadin kai na yankin da tsaro.
Taron na zuwa a lokacin da shugaba Bola Tinubu da shugaban hukumar ECOWAS su ka gana da shugaban Jamus, Walter Frank Steinmeier.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ministocin ECOWAS sun taru a Abuja
FRCN ta ruwaito cewa shugaban ECOWAS, Omar Touray, ya ce taro ya zo a daidai lokacin da ya dace duba da kalubale masu yawa da yankin ke fuskanta.
Touray ya kuma sanar da Majalisar cewa za a duba batutuwa 30 na musamman da suka shafi cinikayya, tsaro, noma, da zaman lafiya, da sauransu.
An samu ragin kudin kungiyar ECOWAS
Shugaban na ECOWAS ya ce a cikin shekaru shida da suka gabata, kudin da ake bayarwa daga kasashe mambobi sun ragu da 40%. Ya jinjina wa gudanar da zabe cikin lumana a bana a kasashen Laberiya, Senegal, Togo da Ghana.
ECOWAS na zawarcin Nijar, Mali da Burkina Faso
A baya mun ruwaito cewa shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu ya bayyana yadda ake ƙoƙarin jawo ra'ayin ƙasashen Nijar, Mali da Burkina Faso su dawo cikin ƙungiyar ECOWAS.
Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya shaida wa shugaban ƙasar Jamus, Walter Frank Steinmeier cewa ana kokarin amfani da diflomasiyya, har su janye ficewar da su ka yi a baya.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng