Majalisar Dattawa ba da Umarni kan Rusau a Abuja, Za Ta Gayyaci Wike
- Majalisar dattawan Najeriya ta shiga cikin batun rushe gine-ginen da ake yi a babban birnin tarayya Abuja
- Majalisar dattawan ta kafa kwamitin da zai yi bincike kan rusau ɗin da ake yi wanda ya jawo mutane da dama suka rasa muhallinsu
- Kwamitin da majalisar ta kafa zai kuma gayyaci ministan babban birnin tarayya Abuja, domin yin bayani kan dalilin rushe gine-ginen
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
FCT, Abuja - Majalisar dattawan Najeriya ta taɓo batun rushe gine-ginen da ake yi a birnin tarayya Abuja.
Majalisar dattawan ta kafa kwamitin da zai yi bincike kan lamarin a ranar Alhamis, 12 ga watan Disamban 2024.
Majalisar dattawa za ta gayyaci Wike
Tashar Channels tv ta rahoto cewa kwamitin da aka kafa, zai gayyaci ministan babban birnin tarayya Abuja, Nyesom Wike.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Za a gayyato Wike ne domin yin bayani kan dalilin yin rusau ɗin, wanda ya raba mutane da dama da gidajensu.
Sanatan birnin tarayya Abuja, Ireti Kingibe, ce ta gabatar da ƙudirin hakan a gaban majalisar dattawan.
Ƙudirin ya nuna damuwa kan rusau ɗin da ake yi a Abuja tare da yin kiran a gaggauta dakatar da ci gaba da rushe gine-ginen.
Majalisar dattawa ta yanke shawarar kafa wani kwamitin bincike da zai binciki rusau ɗin da ake yi, tare da bayar da rahotonsa a kan lokaci.
Majalisa ta gayyaci shugaban kamfani
Majalisar ta kuma gayyaci manajan darakta na kamfanin Julius Berger Nigeria PLC, bisa ƙin amsa gayyatar da kamfanin ya yi domin bayar da cikakkun bayanai kan aikin babbar hanyar Odukpani-Itu, rahoton Tribune ya tabbatar.
Babbar hanyar Odukpani zuwa Itu tana cikin jihar Cross River da kuma jihar Akwa Ibom.
Majalisa ta amince a kafa jami'a
A wani labarin kuma, kun ji cewa majalisar dattawan Najeriya ta amince a kafa sabuwar jami'a a jihar Plateau da ke yankin Arewa ta Tsakiya.
Majalisar ta amince da ƙudirin da ya kafa sabuwar jami'ar ma'adanai a jihar Plateau, yayin zamanta na ranar Talata, 10 ga watan Disamban 2024.
Asali: Legit.ng