Tinubu Ya Fadi Shirinsu a kan Nijar da Sauran Kasashen Afrika da Suka Bar ECOWAS

Tinubu Ya Fadi Shirinsu a kan Nijar da Sauran Kasashen Afrika da Suka Bar ECOWAS

  • Shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu ya tattauna da takwaransa na Jamus, Frank-Walter Steinmeier kan muhimman batutuwa
  • Ya shaidawa Mista Steinmeier irin dabarun da ake amfani da su wajen jawo hankalin ƙasashen Sahel su dawo cikin ECOWAS
  • Ƙasashen Mali, jamhuriyyar Nijar da Burkina Faso sun fice daga ƙungiyar ECOWAS bayan an yi juyin mulki

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

FCT Abuja - Shugaba Bola Tinubu ya faɗi hanyar da ƙungiyar ECOWAS ta ke bi domin lallaɓa ƙasashen Nijar, Mali da Burkina Faso su dawo cikin ƙungiyar.

Tinubu, wanda shi ne shugaban ECOWAS, ya yi wannan bayani ne yayin da ya karɓi bakuncin shugaban ƙasar Jamus, Frank-Walter Steinmeier, a Abuja.

Tinubu
ECOWAS na son ƙasashen Sahel da su ka fice daga cikinta su dawo Hoto: @officialABAT
Asali: Twitter

Jaridar The Nation ta ruwaito cewa shugaba Tinubu ya faɗi dabaru biyu da zai yi amfani da su wajen shawo kan ƙasashen uku.

Kara karanta wannan

Kudirin haraji: Matawalle ya ja kunnen masu sukar Tinubu, ya fadi amfanin yin gyaran

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

ECOWAS: Dabarun shawo kan ƙasashen Sahel

Jaridar The Cable ta wallafa shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu ya ce zai yi amfani da hikima da diflomasiyya wajen dawo da Mali, Jamhuriyar Nijar, da Burkina Faso cikin ƙungiyar ECOWAS.

Shugaba Tinubu ya bayyana cewa shugabannin ƙasashen sun yi jinkiri wajen gabatar da shirin mika mulki ga farar hula kamar yadda aka sa rai.

Shawarar shugaban Jamus ga kungiyar ECOWAS

Shugaban Jamus ya ce dawowar ƙasashen Nijar, Mali da Burkina Faso cikin ECOWAS zai yi tasiri kan tattalin arziki da tsaron yankin.

Steinmeier ya bukaci Tinubu da ya tanadi “shirin ko-ta-kwana" domin haɗin gwiwar tattalin arziki nan gaba yayin da ake jan kafa wajen dawo da ƙasashen.

Shugaban Jamus zai gana da shugabannin ECOWAS

A baya, kun ji cewa shugaban kasar Jamus, Frank-Walter Steinmeier ya kawo ziyarar kwanaki uku zuwa Najeriya, ya gana da Bola Ahmed Tinubu a kan batutuwa da dama.

Kara karanta wannan

Zaben 2027: Atiku ya maida martani bayan Akume ya bukaci ya hakura da takara

Bayan ganawar sirri da shugaban ƙasa, Tinubu Mista Steinmeier ya kuma gana da jagororin ECOWAS da wasu daga cikin shugabannin ƴan kasuwa da jagori a ɓangaren al'adu.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.