An Kama 'Yan Ta'addar da Suka Tunkari Kasuwa da Bindigogi domin kai Hari
- Rundunar Sojojin Najeriya ta dakile wani hari da ‘yan bindiga suka shirya kaiwa a Kudancin Jihar Taraba
- Sojoji sun kama wasu mutane biyu, Terry Waapara da Tobaya Tekura, dauke da bindigogin AK-47 da tarin harsasai
- An samu nasarar ne ta hanyar samun bayanan sirri, wanda ya kai ga aiwatar da sintiri da wasu ayyukan soji a yankin
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Taraba - Rundunar sojojin Najeriya ta bayyana nasarar da ta samu kan wasu 'yan bindiga a Kudancin jihar Taraba.
A wata sanarwa da sojoji suka fitar ranar Alhamis, an bayyana cewa rundunar ta 6 ne da ke karkashin Operation Whirl Stroke (OPWS) ta samu nasara kan miyagun.
Jaridar Vanguarda ta wallafa cewa sojojin sun kama mutane biyu da ake zargi suna cikin miyagun da suka yi nufin kai hari a wata kasuwa.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Sojoji sun dakile hari a Kudancin Taraba
A ranar 11 ga Disamba, 2024, sojoji suka samu bayanan sirri kan shirin wasu 'ya ta'adda na kai hari a Kudancin Taraba.
Daga samun labarin, sojojin suka gaggauta daukar matakan sintiri da kai farmaki domin dakile shirin 'yan ta'addar.
An kama 'yan ta'addar da suka nufi kasuwa
A yayin farmakin sojojin, an kama Terry Waapara da Tobaya Tekura a kauyen Adu yayin da suke kokarin shiga kasuwar Chachanji.
Rahotanni sun nuna cewa 'yan bindigar suna shirin aiwatar da ta’addanci ne a kasuwar ciki har da garkuwa da mutane.
Makaman da aka kwato wajen 'yan ta'adda
Rahoton Channels Television ya nuna cewa sojojin Najeriya sun kwace bindigogi kirar AK-47 guda biyu da tarin harsasai daga hannun miyagun.
Yanzu haka wadanda ake zargin suna hannun hukuma kuma ana ci gaba da bincike domin gano sauran ‘yan ta'addar da suke aiki tare.
An kama babban dan bindiga a Filato
A wani rahoton, kun ji cewa dakarun rundunar sojin Najeriya sun wargaza mafakar 'yan ta'adda a karamar hukumar Bassa tare da cafke wani dan bindiga.
An kama abokin ta'addancin dan bindigar mai suna Alhassan Samaila tare da kwace tarin harsasai da suka boye a wata jarka.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng