Yadda Babban Sarkin Yarabawa Ya kai wa Buhari Ziyarar Ban Girma a Daura

Yadda Babban Sarkin Yarabawa Ya kai wa Buhari Ziyarar Ban Girma a Daura

  • Mai martaba Ooni na Ife, Oba Adeyeye Ogunwusi, ya kai ziyara ga tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari a Daura
  • Rahotanni sun nuna cewa Oba Adeyeye Ogunwusi ya kuma ziyarci fadar sarkin Daura tare da Buhari kafin barin garin
  • Shugaba Muhammadu Buhari na ci gaba da karbar manyan mutane yayin da suke kawo masa ziyara bayan barin mulki

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Katsina - Babban basarake a kasar Yarabawa, Oba Adeyeye Enitan Ogunwusi ya kai ziyarar ban girma ga tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari.

An ruwaito cewa Ooni na Ife, Oba Adeyeye Enitan Ogunwusi ya ziyarci shugaba Buhari ne a gidansa na Daura a ranar Laraba.

Buhari
Ooni na Ife ya ziyarci Buhari a Daura. Hoto: Bashir Ahmad
Asali: Facebook

Legit ta tattaro bayanai kan ziyarar be a cikin wani sako da tsohon hadimin Buhari, Bashir Ahmad ya wallafa a shafinsa na X.

Kara karanta wannan

Shugaban kasar Jamus ya sauka a Najeriya, zai gana da Tinubu

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Rahotanni sun tabbatar da cewa ziyarar ta samu halartar wasu daga cikin tawagar Ooni na Ife, Oba Adeyeye Enitan Ogunwusi.

Ziyarar ban girma ta Ooni na Ife ga Buhari

Ooni na Ife, Oba Adeyeye Ogunwusi, Sarkin Ife, ya kai ziyara ga Buhari domin karfafa zumunci tsakanin shugabannin Najeriya.

Ziyarar ta nuna girma da mutunta tsohon shugaban kasar, wanda ya karbi bakuncin sarkin tare da tawagarsa a gidansa na Daura.

Oonin Ife ya je fadar sarkin Daura

Punch ta wallafa cewa bayan ganawa da Buhari, Ooni na Ife ya samu jagorancin tsohon shugaban kasar zuwa fadar arkin Daura.

Rahotanni sun tabbatar da cewa ziyarar ta samu halartar wasu daga cikin tawagar Ooni na Ife, Oba Adeyeye Enitan Ogunwusi.

“A yau, Ooni na Ife tare da tawagarsa sun ziyarci tsohon Shugaban Kasa Muhammadu Buhari a Daura."
"Tsohon shugaban kasar ya jagoranci Ooni na Ife da tawagarsa zuwa fadar mai martaba sarkin Daura."

Kara karanta wannan

Dattawan Arewa sun soki kalaman Sakataren Gwamnati kan takara da Tinubu a 2027

- Bashir Ahmad

Buhari ya gana da abokansa a Daura

A wani rahoton, kun ji cewa tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari na cigaba da sada zumunci da abokan da suka yi yarinta a makaranta.

Legit ta ruwaito cewa shugaba Buhari ya gana da wasu daga cikin wadanda suka yi makarantar firamare da sakandare da su Katsina.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng