Ana Jimamin Rasuwar Kanwar Gwamna, Mutuwa Ta Sake Ratsa Iyalan Agbu Kefas

Ana Jimamin Rasuwar Kanwar Gwamna, Mutuwa Ta Sake Ratsa Iyalan Agbu Kefas

  • Mutuwa ta sake ratsa iyalan Gwamna Agbu Kefas na jihar Taraba yayin da ake cikin jimamin rasuwar ƙanwarsa, Atsi Kefas
  • Direban mahaifiyar Gwamna Agbu Kefas, ya ce ga garinku nan bayan samun labarin mutuwar Atsi Kefas da aka harba bisa kuskure
  • Wata majiya ta bayyana cewa direban mai suna Abraham ya yanke jiki ya faɗi bayan labarin mutuwar Atsi Kefas ya riske shi

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

FCT, Abuja - Wani abin jimami ya sake aukawa kan iyalan gwamnan jihar Taraba, Dr. Agbu Kefas.

Rahotanni sun bayyana cewa direban mahaifiyar gwamnan, ya faɗi ya rasu bayan samun labarin rasuwar ƴar uwar gwamnan, Atsi Kefas, wacce wani ɗan sanda ya harba bisa kuskure.

Direban iyalan gwamnan Taraba ya rasu
Direban mahaifiyar Gwamna Agbu Kefas ya rasu Hoto: @GovAgbuKefas
Asali: Twitter

Jaridar Daily Trust ta rahoto cewa lamarin ya auku ne a ranar Talata, a gidan T.Y. Danjuma da ke Abuja.

Kara karanta wannan

Hankula sun tashi bayan fashewar wani bam a Borno, bayanai sun fito

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Direba ya rasu bayan jin rasuwar ƙanwar Agbu Kefas

Wata majiya da ke a wurin da lamarin ya faru, ta ce direban mai suna Abraham ya faɗi ne bayan ya yi ihu sakamakon samun labarin rasuwar Atsi Kefas.

Atsi Kefas dai ta rasu ne a wani asibiti da ke birnin tarayya Abuja inda ake kula da lafiyarta bayan harbin da aka yi mata.

"Ina cikin masauki lokacin da abin ya faru. Sai kawai ya faɗi ya mutu bayan jin labarin rasuwar ƴar uwar gwamnan."

- Wata majiya

Direban ne ya tuƙa motar da aka harbi ƙanwar gwamna

Majiyar ta bayyana cewa Abraham, wanda ɗan asalin garin Wukari ne, shi ne ya tuƙa motar wacce aka harbi Atsi Kefas a cikinta, a hanyar Wukari zuwa Kente a ranar 5 ga watan Disamba, 2024.

Abraham ya yi aiki a matsayin direba a ayarin motocin matar gwamnan tun lokacin da Agbu Kefas ya karɓi mulki a shekarar 2023.

Kara karanta wannan

Gwamna ya yi wa'azi ana alhinin rasuwar shugaban karamar hukuma

Ƴan bindiga sun farmaki iyalan gwamnan Taraba

A wani labarin kuma, kun ji cewa ƴan bindiga sun kai hari kan motar da ke ɗauke da mahaifiyar gwamnan Taraba, Agbu Kefas da ƙanwarsa a kan hanyar zuwa Wukari.

Rundunar ƴan sandan jihar Taraba ta tabbatar da kai harin wanda ya shafi iyalan gwamnan a kan hanyar Wukari-Kente a ranar Alhamis, 5 ga watan Disamban 2024.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng