Matatar Dangote Ta Kafa Tarihi, Ta Fara Fitar da Fetur zuwa Makwabciyar Najeriya

Matatar Dangote Ta Kafa Tarihi, Ta Fara Fitar da Fetur zuwa Makwabciyar Najeriya

  • Matatar Dangote da ke birnin Legas ta fara ƙulla yarjejeniya da kamfanin Neptune Oil na kasar Kamaru mai makwabtaka da Najeriya
  • Cimma yarjejeniyar haɗin gwiwar ya sanya matatar ta fara fitar da man fetur zuwa kasar Kamaru
  • Shugaban rukunin kamfanonin Dangote, Alhaji Aliko Dangote ya nuna jindaɗinsa kan wannan haɗin gwiwa da kamfanin na ƙasar Kamaru

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Legas - Matatar dangote ta fara fitar da man fetur zuwa ƙasar Kamaru mai makwabtaka da Najeriya.

An cimma hakan ne tare da haɗin gwiwa tsakanin matatar Dangote da kamfanin Neptune Oil, babban kamfanin samar da makamashi a ƙasar Kamaru.

Matatar Dangote ta fitar da fetur zuwa Kamaru
Matatar Dangote ta fara fitar da fetur zuwa kasar Kamaru Hoto: Bloomberg
Asali: UGC

Jaridar Daily Trust ta ce fara fitar da man fetur ɗin shi ne na farko daga matatar Dangote zuwa ƙasar Kamaru.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Matatar Dangote ta fitar da fetur zuwa Kamaru

Kara karanta wannan

Wasu Gwamnoni 15 sun shiga taro a Abuja kan kudirin harajin Bola Tinubu

A cewar Dangote, wannan ci gaba da aka samu daga haɗin gwiwa tsakanin kamfanonin biyu, ya nuna aniyarsu ta ƙarfafa dangantakar tattalin arziƙi tsakanin Najeriya da Kamaru, rahoton Tribune ya tabbatar.

Shugaban rukunin Dangote, Alhaji Aliko Dangote, ya bayyana cewa haɗin gwiwar da matatar ta yi da kamfanin abin a yaba ne.

"Wannan fitar da man fetur na farko zuwa Kamaru, manuniya ce kan hangen nesanmu na samar da haɗin kai a Afirika ta yadda za ta ci gashin kanta ta fannin makamashi."
"Da wannan ci gaban, mun sanya tubalin samar da lokacin da za a riƙa tace albarkatun Afirika da kuma musayar su a cikin nahiyar domin amfanin jama'armu."

- Alhaji Aliko Dangote

Za a ci gaba da kai fetur zuwa Kamaru

Darakta kuma mamallakin kamfanin Neptune Oil, Antoine Ndzengue, ya bayyana cewa haɗin gwiwa da matatar Dangote ya kawo sauyi ga Kamaru.

Kara karanta wannan

Gwamna zai tura mata 1,000 karatu fannin lafiya, zai raba kwamfutoci miliyan 1

Sanarwar da Dangote ya fitar ta ce fitar da man fetur ɗin a karon farko, bai kawo ƙarshen haɗin gwiwar da ke tsakanin matatar Dangote da kamfanin Neptune Oil ba.

Matatar Dangote ta rage farashin fetur

A wani labarin kuma, kun ji cewa matatar Dangote da ke a jihar Legas ta sauƙaƙa ta hanyar farashin da take siyarwa da ƴan kasuwa man fetur.

Matatar ta Dangote, ta rage farashin fetur ga yan kasuwar daga N990 da ta sanar a farkon watan Nuwambar 2024 da muke ciki zuwa N970.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng