Wani Mummunan Hatsarin Mota Ya Rutsa da Motar Jami'a, An Rasa Rayuka
- Motar bas da ke jigilar ma'aikata a Jami'ar jihar Borno ya gamu da hatsari mai muni ranar Laraba, 11 ga watan Disamba, 2024
- Rahotanni sun nuna cewa hatsarin ya yi sanadiyyar mutuwat mutum uku yayin da wasu 30 ke kwance a asbiti ana masu maganin raunuka
- Ganau sun bayyana cewa wata tirela ce ta ci karo da bas din jami'ar amma jami'an ba da agaji sun kai ɗauki a kan lokaci
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Jihar Borno - Wani mummunn hatsarin mota ya rutsa da motar Bas ta jami'ar jihar Borno da ke Arewa maso Gabashin Najeriya.
Hatsarin wanda ya rutsa da motar Bas ta ma'aikatan jami'a ya yi sanadin mutuwar mutum uku yayin da wasu 30 suka samu raunuka kala daban-daban.
Tirela ta ci karo da motar jami'ar Borno
Jaridar Leadership ta tattaro cewa hatsarin ya afku ne a ranar Laraba, 11 ga watan Disambar 2024 lokacin da wata tirela ta bugi gefen motar bas din jami’ar Borno.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Nan take dai aka garzaya da wadanda lamarin ya rutsa da su zuwa asibitin kwararru na Umaru Shehu, inda suke samun kulawar likitoci.
Shaidun gani da ido sun bayyana cewa hatsarin ya haifar da mummunar barna ga motar bas din jami'ar, kamar yadda The Cable ta rahoto.
Jami'an agajin gaggawa sun kai ɗauki
Sai dai shaidun da lamarin ya faru a kan idonsu sun tabbatar da cewa jami'an ba da agaji sun kai ɗauki a kan lokaci kuma sun kwashe waɗanda lamarin ya shafa zuwa asibiti.
An ruwaito cewa a halin yanzu likitoci na ci gaba da ƙoƙarin kula da wadanda suka jikkata yayin da aka kwashe gawarwakin wadanda suka mutu domin a yi masu jana'iza.
Har kawo yanzu dai babu wata sanarwa a hukumance daga hukumar kiyaye haɗurra watau FRSC, ƴan sanda ko mahukuntan jami'ar Borno kan lamarin.
Mutum 16 sun mutu a hatsarin mota
A wani labarin, an ji cewa hatsarin mota ya laƙume rayukan mutum 16 a kan gadar Njaba da ke karamar hukumar Njaba a jihar Imo ranar Talata.
Ganau da lamarin ya faru a kan idonsu sun ce motar hayan ta kufcewa direban, ta bugi gefen gadar sannan ta faɗa cikin kogi
Asali: Legit.ng