"Mutane Za Su Ji Daɗi," An Buƙaci Tinubu Ya Dawo da Farashin Fetur N300 na Watanni 2

"Mutane Za Su Ji Daɗi," An Buƙaci Tinubu Ya Dawo da Farashin Fetur N300 na Watanni 2

  • An buƙaci shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu ya dawo da farashin litar man fetur N300 domin ƴan Najeriya su yi kirsimeti cikin farin ciki
  • Tsohon mataimakin shugaban PDP na ƙasa, Bode Gearge ne ya yi wannan kira, ya ce Tinubu na iya fito da tsarin neman tallafin rage farashin
  • Jigon PDP ya buƙaci sauke farashin daga nan zuwa watan Janairu, 2025, ya ce magidanta za su yi wa shugaban kasa addu'a idan ya sauƙaƙa masu

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Abuja - Tsohon mataimakin shugaban jam’iyyar PDP na kasa, Cif Bode George, ya yi kira ga shugaban kasa, Bola Tinubu da ya rage farashin man fetur a lokacin kirsimeti.

Bode George ya roƙi Shugaba Tinubu ya tausaya ya sauke farashin litar man fetur daga sama da N1,000 zuwa N300 kacal a tsakanin watannin Disamba da Janairu.

Kara karanta wannan

Tsohon mai ba Jonathan shawara ya fadi abin da zai faru da tattalin Najeriya kwanan nan

Bode George da Bola Tinubu.
Bode George ta bukaci Tinubu ya rage farashin litar fetur zuwa N300 Hoto: Chief Bode George, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu
Asali: Facebook

A cewarsa, dawo da litar mai N300 zai taimakawa ƴan Najeriya su yi bukukuwan kirsimeti cikin walwala da farin ciki, kamar yadda Daily Trust ta rahoto.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Nawa ake sayar da litar fetur a Najeriya?

Legit Hausa gano cewa a halin yanzu ana sayar da litar man fetur a tsakanin N1,100 da kuma N1,200 a fadin kasar nan sakamakon cire tallafin mai.

A lokacin da aka rantsar da Tinubu a 2023 ya sanar da tuge tallafin wanda ya janyo tashin farashi mai farko daga N198 zuwa N560, ya ci gaba da tashi zuwa yanzu.

Da yake hira da manema labarai, George ya roƙi Tinubu ya rage farashin man fetur daga yanzu zuwa watan Janairu domin rage abin da ya kira “fushi da yunwa” a kasar.

George ya roki Tinubu ya sauke farashin fetur

Ya bayyana cewa Shugaban kasa na iya fito da wani tsarin rage kudin litar man da kuma neman tallafi daga masu kishin kasa da masu hannu da shuni.

Kara karanta wannan

Karfin Naira: Ƴan canji sun lissafa abubuwa 3 da suka jawo dalar Amurka ta karye

"Idan ya yi wannan, tamkar ya tura saƙon farin ciki da murna ne ga kowane gida a bukukuwan kirsimeti da sabuwar shekara,"

- Bode George.

Jigon PDP ya ce Uwargidan shugaban kasa, Sanata Oluremi Tinubu, za ta iya bayar da gudunmawa wajen rage farashin man fetur zuwa N300, rahoton Vanguard.

Ya nanata cewa rage farashin man fetur zai rage tsadar kayan abinci kuma ‘yan Najeriya za su yi bukukuwan Kirsimeti cikin jin dadi tare da yin addu’a ga shugaban kasa.

IPMAN ta fara ɗauko mai daga matatar Ɗangote

Ku na da labarin ƙungiyar dillalan man fetur ta ƙasa mai zaman kanta (IPMAN), ta fara dakon man fetur kai tsaye daga matatar mai ta Ɗangote da ke Legas.

Lamarin ya tabbata ne bayan kungiyar ta sha tattauna wa da matatar domin ba ta damar sayo fetur kai tsaye ba tare da NNPCL ya shiga tsakani ba.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262