Sarki Sanusi II Ya Yanke Shawara bayan Jami'an Tsaro Sun Hana Shi zuwa Bichi
- Muhammadu Sanusi II ya sha alwashin raka hakimin Bichi Munir Sanusi Bayero zuwa yankinsa cikin lumana a nan gaba
- Mai martaba sarkin Kano na 16 ya faɗi haka ne da ya karɓi bakunci tawagar masarautar Bichi a fadarsa da ke Kano ranar Laraba
- Ranar Juma'a da ta gabata Sarki Sanusi ya shirya yi wa hakimin rakiya amma jami'an tsaro suka kewaye fadarsa suka hana shi tafiya
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Kano - Mai martaba sarkin Kano na 16, Muhammadu Sanusi II ya bayyana cewa ba abin da zai hana shi raka Wamban Kano kuma hakimin Bichi masarautarsa.
Sanusi II ya tabbatarwa al'ummar ƙaramar hukumar Bichi cewa hakiminsu, Munir Sanusi Bayero zai kama aiki a masarauta nan ba da jimawa ba.
Sanusi II ya sha alwashin raka hakimin Bichi
Basaraken ya yi wannan furucin ne yayin da tawagar masarautar Bichi da ta ƙunshi sarakuna, malamai da dattawa ta kai masa ziyara a fadarsa, rahoton Punch.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Tawagar masarautar karkashin shugaban karamar hukumar Bichi, Alhaji Hamza Sule Maifata ta ziyarci sarkin ne domin jaddada mubaya'a.
Mai martaba sarkin Kano ya shaida masu cewa nan bada jimawa ba zai sake sanya ranar da za a yi wa sabon hakimin rakiya zuwa yankinsa, Tribune ta rahoto.
Abin da ya kawo wa sarki Sanusi II cikas
Idan ba ku manta ba, Sanusi II ya shirya raka Munir Sanusi zuwa masarautar Bichi ranar Juma'a, kwatsam jami'an tsaro suka mamaye fadarsa.
Jami'an tsaron da suka hada da ƴan sanda da dakarun DSS sun kewaye fadar, sannan suka hana shiga da fita, lamarin da ya kawo cikas ga rakiyar hakimin.
A cewar wasu majiyoyi daga fadar, zuwan dakarun ƴan sanda da DSS ya jawo cikas ga rakiyar sabon hakimin, wanda kuma har yanzu ba a san dalilin haka ba.
Da yake jawabi ga tawagar masarautar Bichi yau Laraba, Muhammadu Sanusi ya ce:
"Ina tabbatar maku da cewa za mu sake sa rana mu kawo maku hakiminku kuma komai zai tafi cikin lumana."
Masarautar Bichi ta amince da naɗin Hakimi
A wani rahoton, kun ji cewa majalisar masarautar Bichi ta kai ziyarar nuna goyon baya da mubaya'a ga mai martaba sarkin Kano na 16, Muhammadu Sanusi II.
Wakilan masarautar Bichi sun jaddada cewa suna tare da matakin Sanusi II na naɗa masu sabon hakimi watau Munir Sanusi.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng