Sarki Sanusi II Ya Samu Goyon Baya kan Naɗin Hakimin Bichi duk da Abin da Ya Faru

Sarki Sanusi II Ya Samu Goyon Baya kan Naɗin Hakimin Bichi duk da Abin da Ya Faru

  • Majalisar masarautar Bichi ta kai ziyarar nuna goyon baya da mubaya'a ga mai martaba sarkin Kano na 16, Muhammadu Sanusi II
  • Wakilan masarautar Bichi sun jaddada cewa suna tare da matakin Sanusi II na naɗa masu sabon hakimi watau Munir Sanusi
  • Sarkin ya gode masu bisa goyon bayan da suka nuna masa, sannan ya ba su tabbacin cewa zai sake sa ranar rakiyar hakimin

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Kano - Masarautar Bichi ta jaddada mubaya'a da kuma amincewa da naɗin sabon hakimin da mai martaba sarkin Kano na 16, Muhammadu Sanusi II ya yi.

Idan ba ku manta ba Sarki Sanusi II ya naɗa Munir Sanusi Bayero a matsayin hakimin Bichi.

Muhammadu Sanusi II
Masarautar Bichi ta amince da nadin sabon hakimi, Munir Sanusi Hoto: @masarautarkano
Asali: Twitter

Tribune Nigeria ta tattaro cewa a yau Laraba wakilan masarautar Bichi suka kai wa Sarki Sanusi ziyara domin jaddada mubaya'arsu a fadarsa da ke Kano.

Kara karanta wannan

Sarki Sanusi II ya yanke shawara bayan jami'an tsaro sun hana shi zuwa Bichi

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Masarautar Bichi ta kai ziyara fadar sarki

Shugaban karamar hukumar Bichi, Hamza Sule Maifata, babban limami, Mallam Lawan Abubakar da dattawa na cikin tawagar masarautar Bichi da ta kai ziyara ga sarki.

Majalisar Masarautar Bichi ta jaddada biyayyarta ga Sarki Muhammadu Sanusi II, inda ta nuna cewa tana tare da mai martaba kan naɗin sabon hakimi.

Muhammadu Sanusi II ya godewa masarautar Bichi

Da yake jawabi yayin ziyarar, Sanusi II ya gode wa majalisar bisa goyon bayan da suka ba shi, ya kuma ba su tabbacin cewa za a gudanar da nadin sabon hakimin lami lafiya.

Sarkin ya kara nanata muhimmancin zaman lafiya da yawaita addu'o'i a kowane hali mutane suka tsinci kansu a ciki.

Wannan dai na zuwa ne bayan matakin da jami'an ƴan sanda da DSS suka ɗauka na hana sarkin raka hakimin zuwa ƙasarsa a makon jiya.

Muhammadu Sanusi II ya shaidawa wakilan masarautar Bichi cewa zai sake sa rana nan gaba domin kawo masu sabon hakimin, kamar yadda Punch ta kawo.

Kara karanta wannan

A karshe, Sarkin Kano ya yi magana kan mamaye fadarsa da jami'an tsaro suka yi

Meyasa jami'an tsaro suka kewaye fadar Sanusi?

Rahoto ya gabata cewa Sarkin Kano na 16, Muhammadu Sanusi II, ya yi magana kan abin da ya faru a fadarsa da ke Ƙofar Kudu a makon jiya.

Sanusi II ya ce har yanzu masarautar Kano ba ta da masaniya kan dalilan da suka sanya jami’an tsaro suka mamaye fadar ranar Juma'a.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262