A Karshe, Sarkin Kano Ya Yi Magana kan Mamaye Fadarsa da Jami'an Tsaro Suka Yi
- Mai Martaba sarkin Kano, Alhaji Muhammadu Sanusi II ya ce har yanzun ba shi da masaniyar dalilin jami'an tsaro na mamaye fadarsa
- Sanusi II ya faɗi haka ne yayin da ya karbi bakuncin wakilan masarautar Bichi da suka kai masa ziyara ranar Laraba
- Sarkin ya ce koma maye dalilin waɗanda suka sa a mamaye fadar, ba zai hana shi raka Wamban Kano hakimin Bichi masarautarsa ba
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Kano - Sarkin Kano na 16, Muhammadu Sanusi II, ya yi magana kan abin da ya faru a fadarsa da ke Ƙofar Kudu a makon jiya.
Sanuai II ya ce har yanzu masarautar Kano ba ta da masaniya kan dalilan da suka sanya jami’an tsaro suka mamaye fadar ranar Juma'a da ta gabata.
Jaridar Daily Trust ta ruwaito yadda dakarun ‘yan sanda da jami’an hukumar DSS suka toshe hanyar zuwa fadar sarkin, kuma suka hana kowa shiga ko fita.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Menene dalilin mamaye fadar sarkin Kano?
Duk da jami'an tsaro ba su faɗi dalilin kewaye gidan sarkin ba, amma wasu majiyoyi sun ce hakan ba zai rasa alaƙa da naɗin Wamban Kano hakimin Bichi, Munir Sanusi ba.
A ranar da lamarin ya faru, Sarki Sanusi II ya shirya raka sabon Wamban Kano zuwa masarautarsa a Bichi kwatsam ƴan sanda suka hana.
Tun a lokacin gwamnatin Kano ta fusata, inda ta zargi gwamnatin tarayya da hannu a matakin da jami'an tsaron suka ɗauka na mamaye fadar sarki.
Sarki Sanusi II ya magantu kan lamarin
Da yake tsokaci kan abin da ya faru yau Laraba lokacin da ya karɓi bakuncin wakilai daga masarautar Bichi, Sarki Sanusi ya ce har yanzu bai san dalili ba.
Muhammadu Sanusi II ya ce:
"Abin da ya faru ɗauke hankali kawai ake so a yi, har yanzun ba mu san dalilin da ya sa hakan ta faru ba kuma waɗanda suka sa a yi ba su faɗa mana dalili ba."
"Wannan ba zai hana mu komai ba, ina tabbatar maku da cewa za mu sake sa rana mu kawo maku hakiminku kuma komai zai tafi cikin lumana da zaman lafiya."
Sarkin Kano ya ja kunnen masu sarauta
A wani labarin an ji cewa Muhammadu Sanusi II ya gargaɗi masu riƙe da sarautun gargajiya da su guji abin da zai raba su da rawaninsu.
Sanusi II ya bayyana cewa masarauta ba za ta lamunci duk wani basarake da ke lakadawa matarsa duka ba.
Asali: Legit.ng