Majalisar Dattawa Ta Ayyana Kujerar Gwamna a Matsayin Wanda Babu Kowa a Kai

Majalisar Dattawa Ta Ayyana Kujerar Gwamna a Matsayin Wanda Babu Kowa a Kai

  • A karshe Majalisar dattawa ta ayyana kujerar Gwamna Okpebholo ta sanatan Edo ta Tsakiya a matsayin wanda babu kowa a kanta
  • Shugaban majalisar, Godswill Akpabio ne ya bayyana hakan a zaman da sanatoci suka shiryawa gwamnan a ranar Laraba, 11 ga watan Disamba, 2024
  • Kujerar Okpebholo ta Sanata mai wakiltar Edo ta Tsakiya ta zama babu kowa ne bayan nasarar da ya samu da rantsar da shi a matsayin gwamnan Edo

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Abuja - Majalisar dattawan Najeriya a ranar Laraba ta bayyana kujerar Gwamna Monday Okpebolo a matsayin wanda ba kowa.

Majalisar dattawan ta kuma bukaci hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC) ta gudanar da zabe a mazaɓarsa domin cike gurbin.

Akpabio da Monday Okpebholo.
Majalisar dattawa ta nemi INEC ta shirya zaben cike gurbin sanatan Edo ta Tsakiya Hoto: Nigeria Senate
Asali: Twitter

Kujerar gwamna a Majalisa ta zama babu kowa

Kujerar Okpebhoho, sanata mai wakiltar Edo ta Tsakiya ta zama babu kowa ne bayan nasarar da ya samu a zaɓe da kuma rantsar da shi a matsayin gwamnan Edo.

Kara karanta wannan

Majalisa ta ayyana kujerar mataimakin gwamna a matsayin wanda babu kowa a kai

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

The Nation ta ce Monday Okpebholo ya ajiye kujarar sanatan Edo ta Tsakiya, ya shiga neman takara kuma Allah ya ba shi nasarar zama gwamnan Edo a inuwar APC.

Hakan ya sa a zaman yau Laraba, Majalisar dattawa ta ayyana kujerar sanatan Edo ta tsakiya a matsayin babu kowa ma'ana INEC ta shirya zaɓen cike gurbi.

Majalisar Dattawa ta buƙaci INEC ta cike gurbin Sanata

Shugaban majalisar dattawa, Sanata Godswill Akpabio ne ya bayyana hakan a zama na musamman da aka shiryawa Gwamna Okpebholo.

Akpabio ya roƙi Monday Okpebholo da ya ci gaba da ayyukan alherin da aka san shi da su yayin sauke nauyin da al'umma suka ɗora masa a matsayin gwamnan Edo.

Shugaban marasa rinjaye, Sanata Abba Moro ne ya bukaci Majalisa ta ayyana kujerar Okpebholo da babu kowa bisa tanadin kundin tsarin mulkin Najeriya.

Sai dai ba tare gardana ba gaba ɗaya ƴan Majalisar suka amince kuma Akpabio ya buga guduma tare da ayyana kujerar sanatan Edo ta Tsakiya da ba kowa a kai.

Kara karanta wannan

'Bai iya sata ba ne': APC ta kare gwamna da ya gagara yin lissafin kasafin kudi

Majalisa ta ayyana cewa babu kowa a kujerar Idahosa

Ku na da labarin Majalisar wakilai ta ayyana kujerar mataimakin gwamnan jihar Edo, Dennis Idahosa, a matsayin wanda babu kowa a kanta.

Kakakin majalisar, Rt. Hon. Abbas Tajudeen ya ayyana kujerar Idahosa mai wakiltar mazaɓar Ovia daga jihar Edo, a matsayin wacce babu kowa a kanta ne a ranar Laraba.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262