Ana Jimamin Mutuwar Ciyaman, Mataimakin Karamar Hukuma Ya Rasu

Ana Jimamin Mutuwar Ciyaman, Mataimakin Karamar Hukuma Ya Rasu

  • Mataimakin shugaban karamar hukumar Ikale ta Arewa a jihar Ondo, Owonola Emmanuel Abiodun ya rasu bayan fama da rashin lafiya
  • Gwamna Lucky Orimisan Aiyedatiwa ya bayyana rasuwar Owonola Emmanuel Abiodun a matsayin babban rashi ga jihar Ondo
  • Hakan na zuwa ne yayin da wani shugaban karamar hukuma ya rasu a jihar Neja a sanadiyyar mummunan hadarin mota

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Ondo - Gwamnan Jihar Ondo, Lucky Orimisan Aiyedatiwa ya bayyana babban rashin da jihar Ondo ta yi sakamakon rasuwar Owonola Emmanuel Abiodun.

Rahotanni sun nuna cewa Owonola Emmanuel Abiodun ne mataimakin shugaban karamar hukumar Ikale ta Arewa.

Jihar Ondo
Mataimakin shugaban karamar hukuma ya rasu a Ondo. Hoto: Ebenezer Adeniyan
Asali: Facebook

Hadimin gwamna Aiyedatiwa, Ebenezer Adeniyan ya wallafa a Facebook cewa Hon. Owonol ya rasu ne a ranar Talata bayan fama da rashin lafiya.

Kara karanta wannan

Gwamna ya yi wa'azi ana alhinin rasuwar shugaban karamar hukuma

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Gwamna Aiyedatiwa ya yi jimamin rashin Abiodun

Rahotanni sun tabbatar da cewa gwamna Lucky Orimisan Aiyedatiwa ya ce ji ji zafi matuƙa da jin labarin rasuwar Owonola Emmanuel Abiodun.

"Ya kasance matashi mai kwazo wanda ya yi wa jihar Ondo hidima ta hanyar gaskiya da rikon amana ba tare da tsoro ba.”

- Gwamna Lucky Orimisan Aiyedatiwa

Gwamnan ya ƙara da cewa rasuwar marigayin babban rashi ne ga yankin Ikale da kuma jihar Ondo baki ɗaya.

Jajircewar marigayi Abiodun a jihar Ondo

Gwamnan ya bayyana cewa marigayin ya kasance wani ɓangare da ke taimaka masa wajen bai wa matasa damar shiga gwamnati.

“Owonola ya kasance matashi mai kishin gaskiya da ya tsaya tsayin daka wajen kawo cigaba ga al’umma.”

- Gwamna Lucky Orimisan Aiyedatiwa

Gwamna Aiyedatiwa ya ƙara da cewa marigayin ya bar ɗimbin alheri da ayyuka na ƙwarai da za a riƙa tunawa da shi.

Kara karanta wannan

Gwamna zai tura mata 1,000 karatu fannin lafiya, zai raba kwamfutoci miliyan 1

A madadin gwamnatin jihar Ondo, gwamnan ya miƙa sakon ta’aziyya ga iyalan marigayin, abokanansa, da duk waɗanda suke da alaka da shi.

Ciyaman ya rasu a jihar Neja

A wani rahoton, kun ji cewa an yi babban rashi a jihar Neja yayin da aka sanar da rasuwar shugaban ƙasar hukumar Katcha, Danlami Abdullah Saku.

Hon. Danlami Abdullah Saku ya rasu ne sakamakon wani hadarin mota da ya rutsa da shi a titin Minna-Suleja a daren ranar Talata.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng