Kwana Ya Kare: Wani Shugaban Al'umma Ya Ƙara Mutuwa a Hannun Sojojin Najeriya

Kwana Ya Kare: Wani Shugaban Al'umma Ya Ƙara Mutuwa a Hannun Sojojin Najeriya

  • Mutanen garin Okuama a jihar Delta sun sake shiga jimami karo na biyu sakamakon rasuwar ɗaya daga cikin shugabanninsu
  • Ma'ajin garin Okuama ya mutu kwanaki shida bayan samun labarin rasuwar babban shugaban garin a hannun dakarun sojoji
  • Matasan garin sun nuna fushinsu kuma sun ba gwamnatin tarayya wa'adin mako guda ta ɗauki matakin da ya dace

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Delta - Al'ummar garin Okuama da ke ƙaramar hukumar Ughelli a jihar Delta sun sake shiga jimami da alhinin rasuwar ɗaya daga cikin jagororinsu.

Ma'ajin garin Okuama, Dennis Okugbaye ɗan kimanin shekara 81 a duniya ya mutu a hannun dakarun sojojin Najeriya.

Taswirar jihar Delta.
Wani shugaban al'ummar garin Okuama a jihar Delta ya cika a hannun sojoji Hoto: Legit.ng
Asali: Original

Mutuwar Okugbaye ta zo ne kwanaki shida bayan da aka ce shugaban Okuama gaba ɗaya, Pa James Oghoroko, ya mutu a irin wannan yanayi a wurin sojoji.

Kara karanta wannan

Gwamna zai tura mata 1,000 karatu fannin lafiya, zai raba kwamfutoci miliyan 1

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Delta: Wani shugaba a Okuama ya mutu

Fasto Akpos Okugbaye, dan marigayi ma'ajin ne ya sanar da rasuwar mahaifinsa ranar Talata, kamar yadda Punch ta ruwaito.

Shugabannin biyu tare da wasu da suka hada da Farfesa Arthur Ekpekpo, Cif Belvis Adogbo, Misis Mabel Owhemu, da Mista Dennis Malaka, sun shiga hannun sojoji ne tsakanin 18 zuwa 20 ga watan Agustan 2024.

An kama mutanen ne sakamakon kisan gillar da aka yi wa sojoji 17 a garin Okuama lokacin da suka je sasanta rikicinsu da kauyen Okoloba.

Matasa sun ɓarke da zanga-zanga

Mutuwar Pa Okugbaye ta haddasa zanga-zanga a yankin, inda fusatattun matasa suka ba gwamnatin tarayya wa'adin mako guda ta sako masu shugabanninsu.

Masu zanga-zangar suka ce:

"Bayan cikar wa'adin kwanaki bakwai, za mu fito mu toshe wannan kogin, sai dai sojoji da Tinubu su zo su kashe mu domin mu san an shafe Okuama gaba daya.” 

Wani dattijo; Ohwotake Otiero, wanda ya yi magana a madadin masu zanga-zangar, ya yi Allah wadai da mutuwar shugabannin Okuama a tsare a hannun sojoji.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun yi ɓarin wuta a cikin gari, sun yi garkuwa da hadimin tsohon gwamna

Bisa haka ya yi kira ga mahukunta su gaggauta ɗaukar matakin gaggawa da sako sauran wadanda je tsare a hannun jami'an tsaron.

Shugaban Okuama ya mutu a wurin sojoji

A wani labarin, kun ji cewa shugaban Okuama da ke karamar hukumar Ughelli a jihar Delta, Pa James Oghoroko ya mutu a hannun sojoji.

Rahotanni sun nuna cewa shugabannin garin ne suka sanar da hakan a wurin wani zama da suka yi a jihar Delta.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262