Mummunar Gobara Ta Tashi a Fitacciyar Kasuwa, Kayayyakin Miliyoyin Naira Sun Kone

Mummunar Gobara Ta Tashi a Fitacciyar Kasuwa, Kayayyakin Miliyoyin Naira Sun Kone

  • Ƴan kasuwa sun shiga jimami a jihar Legas bayan tashin wata mummunar gobara a fitacciyar kasuwar Alaba Rago
  • Gobarar da ta tashi cikin tsakar dare a kasuwar da ke a unguwar Ojo ta yi sanadiyyar lalata kayayyaki na miliyoyin naira
  • Babban sakataren hukumar ba da agajin gaggawa ta jihar Legas (LASEMA) wanda ya tabbatar da aukuwar lamarin

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Legas - An samu tashin wata mummunar gobara a fitacciyar kasuwar Alaba Rago da ke jihar Legas.

Gobarar wacce ta tashi a kasuwar da ke unguwar Ojo ta lalata kayayyaki na miliyoyin naira.

Gobara ta tashi a Legas
Gobara ta tashi a kasuwar Alaba Rago da ke Legas Hoto: Legit.ng
Asali: Original

Sanarwar da babban sakatare na hukumar bayar da agajin gaggawa ta jihar Legas (LASEMA), Dakta Femi Oke-Osayintolu, ya fitar ta ce gobarar ta tashi ne da tsakar dare, cewar rahoton tashar Channels tv.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Me ya haddasa tashin gobarar?

Kara karanta wannan

An shiga tashin hankali da malamin addini ya bata, an bukaci addu'o'i

Ba a iya gano musabbabin tashin gobarar ba har zuwa lokacin kammala haɗa wannan rahoton.

Gobarar da rahotanni suka ce ta tashi ne da misalin ƙarfe 12:00 na dare, ta lalata kayayyakin da suka kai na miliyoyin naira

A cewar babban sakataren, tawagar hukumar LASEMA sun kai agaji zuwa kasuwar bayan samun kiran gaggawa, rahoton jaridar Vanguard ya tabbatar.

Ya ƙara da cewa da zuwansu wajen suka fara aikin ceto domin hana gobarar yaɗuwa zuwa sauran wurare.

Daraktan hukumar kashe gobara ta jihar Legas, Margaret Adeseye, ta ce an samu nasarar kashe gobarar tare da hana yaɗuwarta.

Karanta wasu labaran kan gobara

Gobara ta lalata shaguna a Nasarawa

A wani labarin kuma, kun ji cewa an samu tashin wata gobara da ta ta ƙona shagunan ɗinki da dama a sabuwar kasuwar zamani da ke Lafiya, babban birnin jihar Nasarawa.

Kara karanta wannan

Bayanai sun fito kan 'dalilin' mamaye fadar Sanusi II, an ce hakan ka iya zama alheri

Rahotanni sun nuna cewa mummunar gobarar ta lalata kayayyaki masu ɗumbin yawa da suka kai darajar miliyoyin Naira.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng