Jami'an Tsaro Sun Yi Dirar Mikiya kan Masu Garkuwa da Mutane, Sun Ceto Mutum 10
- Jami'an tsaro na ƴan sanda sun samu nasarar cafke wasu da ake zargin masu garkuwa da mutane ne a jihar Kogi
- Kwamishinan yaɗa labarai na jihar ya bayyana cewa ƴan sandan sun samu nasarar ne tare da wasu jami'an tsaro masu zaman kansu
- Kingsley Fanwo ya ƙara da cewa an ceto mutane 10 da aka yi garkuwa da su bayan an kai samame maɓoyar miyagun
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Jihar Kogi - Jami’an ƴan sandan Najeriya tare da hadin gwiwar jami’an tsaro masu zaman kansu, sun cafke wasu masu garkuwa da mutane a jihar Kogi.
Jami'an tsaron sun cafke mutane huɗu da ake zargin masu garkuwa da mutane ne tare da ceto mutum 10 da aka sace a yankin Ajaokuta na jihar.
Kwamishinan yaɗa labarai na jihar Kingsley Fanwo ne ya sanar da hakan a wata sanarwa da ya fitar ranar Talata, cewar rahoton jaridar The Punch.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Jami'an tsaro sun cafke masu garkuwa da mutane
Ƙingsley Fanwo ya yabawa tawagar jami'an tsaron kan ɗaukin gaggawa da suka kai, wanda hakan ya yi sanadiyyar ceto mutanen.
Ya bayyana cewa gwamnatin jihar ta ƙulla yarjejeniya da kamfanin tsaro mai zaman kansa, mai suna Base SAN Security Nigeria Limited, domin yin aiki tare da jami’an tsaro wajen magance matsalar tsaro a yankin.
"Bayan samun bayanan sirri an cafke masu garkuwa da mutane, waɗanda suka daɗe suna addabar yankin Ajaokuta, inda suke aikata munanan laifuffuka kamar su garkuwa da mutane, fyaɗe da fashi da makami."
"Samamen da aka kai ya yi sanadiyyar cafke masu garkuwa da mutane guda huɗu tare da ceto mutane 10 da miyagun suka yi garkuwa da su a sassan Kogi ta Gabas."
- Kingsley Fanwo
Kingsley Fanwo ya bayyana cewa mutanen da aka kama suna bayar da haɗin kai ga masu bincike, yayin da ake shirin haɗa mutanen sa aka ceto da iyalansu, rahoton tashar Channels tv ya tabbatar.
Ƴan sanda sun daƙile harin ƴan bindiga
A wani labarin kuma, kun ji cewa rundunar ƴan sandan jihar Kaduna ta sanar da samun nasarori masu yawa kan ƴan bindiga da ƴan fashi da makami.
Jami'an rundunar sun dakile harin ƴan bindiga tare da cafke wasu mutane da ake zargin masu aikata laifin fashi da makami ne a sassan daban-daban na jihar.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng