Gwamna Zulum Ya ba Fannin ilmi Muhimmanci, Ya Fadi Nasarorin da Ya Samu a Borno

Gwamna Zulum Ya ba Fannin ilmi Muhimmanci, Ya Fadi Nasarorin da Ya Samu a Borno

  • Gwamnan jihar Borno, Farfesa Babagana Umara Zulum, ya samu nasarori a fannin yaƙi da yaran da ba sa zuwa makaranta
  • Zulum ya bayyana cewa ya rage adadin yaran da ba sa zuwa makaranta daga sama da miliyan 2.2 zuwa ƙasa da 700,000
  • Gwamnan Borno ya kuma bayyana cewa a cikin shekara biyar ya zuba hannun jari mai yawa a fannin ilmi domin bunƙasa shi

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Borno - Gwamnan jihar Borno, Farfesa Babagana Umara Zulum, ya bayyana nasarorin da gwamnatinsa ta samu a ɓangaren ilmi.

Gwamna Zulum ya bayyana cewa an samu raguwar yaran da ba sa zuwa makaranta a faɗin jihar.

Zulum ya rage yawan yaran da ba sa zuwa makaranta
Gwamna Zulum ya rage adadin yaran da ba sa zuwa makaranta a Borno Hoto: @GovBorno
Asali: Facebook

Gwamna Zulum ya bayyana a shafinsa na Facebook, cewa hakan ya sanya adadin ya ragu daga sama da miliyan 2.2 zuwa ƙasa da 700,000, wanda ya daidai da ragin kaso 70%.

Kara karanta wannan

Gwamna zai tura mata 1,000 karatu fannin lafiya, zai raba kwamfutoci miliyan 1

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Farfesan ya bayyana haka ne a lokacin ƙaddamar da makarantar sakandaren gwamnati da ke Mairi, wanda daraktan bankin duniya a Najeriya, Ndiame Diop, ya halarta.

Gwamna Zulum ya bunƙasa fannin ilmi

Zulum ya ce gwamnatinsa ta zuba jari sosai a fannin ilimi a cikin shekara biyar da suka gabata, da suka haɗa da gina makarantu 104 da gyara ajujuwa 2,931.

Ya ce an kuma raba miliyoyin kayayyaki kamar littattafan rubutu miliyan 20, littattafan karatu miliyan biyu, rigunan makaranta miliyan 15, jakunkunan makaranta 700,000, da sauran kayan koyon karatu.

Gwamnan ya kuma ce ɗalibai 50,000 ne suke cin gajiyar shirin ba da abinci a makarantun jihar a duk shekara yayin da aka samar da kekuna 10,000 domin taimakawa ɗaliban karkara shawo kan ƙalubalen zirga-zirga.

Zulum ya ɗauko gagarumin aiki a Borno

A wani labarin kuma, kun ji cewa gwamnan jihar Borno, Farfesa Babagana Umara Zulum, ya shirya kafa tarihi wajen samar da katafariyar tashar jirgin ƙasa da babu irinta a Arewacin Najeriya.

Kara karanta wannan

Lokaci ya yi: Shugaban karamar hukuma ya riga mu gidan gaskiya a hatsari

Gwamna Babagana Umara Zulum, ya ƙaddamar aikin samar da jirgin ƙasa na cikin gari wanda zai haɗa birnin Maiduguri da kewaye.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng