"Babu Abin da Ya Same Ni," Dan Majalisar Tarayya Ya Musanta Labarin Rasuwarsa

"Babu Abin da Ya Same Ni," Dan Majalisar Tarayya Ya Musanta Labarin Rasuwarsa

  • Dan majalisar wakilan kasar nan, Hon. Yusuf Adamu Gagdi ya kwantar da hankalin magoya baya da masoyansa
  • Ya fito a cikin wani bidiyo tare da karyata labarin rasuwarsa da aka rika wallafawa a wasu shafukan sada zumunta
  • Hon. Yusuf Adamu Gagdi ya kara da bayyana cewa bai dace mutum a dakinsa, ya rika wallafa labarin karya ba

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Plateau - Dan majalisar wakilan kasar nan, Hon. Yusuf Adamu Gagdi ya bayyana yadda ya ci karo da rahotannin rasuwarsa a shafuka daban-daban.

Hon. Gagdi da ke wakiltar mazabar Pankshin/Kanam/Kanke ya shaida yadda ya tsinci labarin, ya bayyana cewa dole ce ta sa ya fito domin karin bayani ga jama'a.

Gadgi
Dan majalisa ya karyata rasuwarsa Hoto: Hon Yusuf Adamu Gagdi
Asali: Facebook

A sakon bidiyo da ya wallafa a shafinsa na Facebook, ya ce ya na cikin koshin lafiya, ko kwarzane bai samu ba ballantana a kai ga batun mutuwa.

Kara karanta wannan

Tsohon mai ba Jonathan shawara ya fadi abin da zai faru da tattalin Najeriya kwanan nan

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

'Dan majalisa ya musanta cewa ya rasu

Hon. Yusuf Adamu Gagdi ya ce ya samu kiran waya daga masoyansa da sauran takwarorinsa na majalisar wakilai da dattawa kan neman tabbacin labarin rasuwarsa.

Ya ce labarin rasuwar da ake yada wa ya taba masoyansa da ke ciki da wajen jiharsa ta Filato, wanda ya sa dole ya fito domin karyata cewa ya koma ga Allah.

Gagdi: 'Dan majalisa ya ba jama'a shawara

Dan majalisar wakilan kasar nan, Yusuf Adamu Gagdi ya shawarci mutanen da ke yada labarin mutuwarsa da cewa su tuba daga yada labaran karya.

Hon. Yusuf Adamu Gagdi ya ce;

"Na fitar da wannan sako ne domin masoya na su san cewa ina cikin koshin lafiya, babu abin da ya same ni.
"Masu yada irin wannan labarin daga gidajensu, su na hada sakonni da hotuna da fatan mutuwa gare ni, ina nan da rai kuma za su sha mamakin abubuwan da zan aiwatar."

Kara karanta wannan

'Ka saɓa da annabi': Malamin Musulunci ya dura kan Sanusi II game da kalamansa

'Dan majalisar APC ya nemi afuwa

A wani labarin, mun ruwaito cewa dan majalisar Kano, Hon. Alhassan Ado Doguwa ya nemi afuwar jam'iyyarsa ta APC bisa wasu kalamai da ke nuna cewa ya na yabon 'yan adawa.

Alhassam Ado Doguwa ya zargi jam'iyyar adawa ta PDP da sauya kalamansa, aka rika yada yadda ya yabi gwamnan PDP a Osun, inda ya yi fatan mulki zai dawo APC a 2026.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.