Gwamna Ya Hango Matsalar da Wasu Jihohi Za Su Shiga idan Kudirin Haraji Ya Zama Doka
- Gwamnan jihar Zamfara ya hango wata matsala da jihohi za su fuskanta idan har aka amince da ƙudirin haraji
- Dauda Lawal ya bayyana cewa idan di ƙudirin ya zama doka, wasu jihohin da ba su da ƙarfi ba za su iya kai labari ba
- Gwamnan ya ce akwai buƙatar a sake duba ƙudirin domin gujewa yin abin da zai cutar da wasu jihohi a nan gaba
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Jihar Zamfara - Gwamnan jihar Zamfara, Dauda Lawal, ya yi magana kan ƙudirin haraji na gwamnatin Bola Tinubu.
Gwamna Dauda Lawal ya bayyana cewa wasu jihohin da ba su da ƙarfi sosai, ba za su kai labari ba idan har aka amince da ƙudirin.
Gwamna Dauda Lawal ya bayyana hakan ne yayin wata tattaunawa da tashar Channels tv a shirinsu na 'Politics Today' a ranar Talata.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Me Gwamna Dauda ya ce kan ƙudirin haraji?
Gwamnan ya bayyana cewa akwai buƙatar a tattauna sosai kan ƙudirin domin ka da a yi abin da zai cutar da wasu jihohi.
Gwamna Dauda Lawal ya nuna cewa wasu jihohi da dama za su sha wahala kafin su iya biyan mafi ƙarancin albashi na N70,000, idan aka amince da ƙudirin.
"Eh batun ƙudirin haraji ya ƙunshi abubuwa da dama, akwai masu kyau da marasa kyau. Muna nazari a kai ta yadda za mu san shawarwarin da za mu ba mutanenmu kan abin da ya dace a yi."
"Gyara fasali a kowane tsari abu ne wanda ba a iya kauce masa, kuma ya kamata a kodayaushe mu tsammaci hakan. Sai dai a ƙoƙarin yin hakan, ya kamata mu yi taka tsantsan ka da mu sa gaggawar yin abin da zai cutar da mu a gaba."
"Saboda haka, na yi amanna cewa ya kamata mu kalli abin da idon basira, mu fahimce shi sannan mu samu matsaya guda ɗaya."
- Gwamna Dauda Lawal
Ƙudirin haraji ya raba ƴan majalisa
A wani labarin kuma, kun ji cewa ƙudurin sauya haraji da ke gaban majalisar dattawa ya janyo cece-kuce mai tsanani a tsakanin sanatoci daga yankin Arewa.
Wasu daga cikin ƴan majalisar dattawan sun nuna goyon baya kan kudurin, yayin da wasu suka nuna adawa da shi tare da bayyana sukarsa a fili.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng