BATTIC: An Sanyawa Katafariyar Cibiya Sunan Bola Tinubu a Abuja
- Hukumar shige da fice ta Najeriya (NIS) ta sanya sunan shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu a cibiyarta ta fasahar zamani da ke birnin Abuja
- Shugabar hukumar, Kemi Nanna Nandap ta bayyana cewa cibiyar za ta taimaka wajen kula da shige da fice tare da kare iyakokin Najeriya
- An tabbatar da cewa cibiyar ta dace da ka'idojin duniya na ICAO da IATA domin inganta tsaro da kula da bayanan 'yan Najeriya da baƙi
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
FCT, Abuja - Hukumar shige da fice ta Najeriya (NIS) ta kaddamar da wata cibiya ta zamani tare da sanya mata sunan shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu.
Shugabar NIS, Kemi Nanna Nandap ta ce cibiyar da aka yi wa lakabi da Bola Ahmed Tinubu Technology Innovation Complex (BATTIC) wata nasara ce a fannin fasaha da tsaro.
The Nation ta wallafa cewa cibiyar za ta taka muhimmiyar rawa wajen kula da shige da fice, tsare iyakokin kasa, da kuma tabbatar da tsaro.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Cibiyar BATTIC ta samu karbuwa a duniya
Cibiyar BATTIC da aka gina a hedkwatar NIS da ke Abuja, ta samu tabbatarwa daga Hukumar Kula da Jiragen Sama ta Duniya (ICAO) da Kungiyar Jiragen Sama ta Kasa da Kasa (IATA).
Kemi Nandap ta ce cibiyar za ta kula da ayyuka masu muhimmanci, ciki har da samar da bayanan sirri na ECOWAS.
Ta kara da cewa fasahar zamani da aka sanya a cibiyar za ta tabbatar da inganci wajen kula da mutanen da ke shiga Najeriya ko barinta.
Bangarori masu muhimmanci na BATTIC
Rahoton TVC ya nuna cewa cibiyar tana da bangarori daban-daban kamar su wuraren kula da bayanan shige da fice, sarrafa biza, da kula da fasfo.
Kemi Nandap ta bayyana cewa kowanne bangare na cibiyar an tsara shi ne bisa matakan zamani domin tabbatar da Najeriya ta zama jagora a harkokin tsaron iyakoki da kula da bayanai.
NIS ta kara kudin fasfo a Najeriya
A wani rahoton, kun ji cewa hukumar shige da fice ta kasa ta fitar da sanarwa kan karin kudin fasfo da zai ba yan Najeriya damar fita kasashen ketare.
An ruwaito cewa NIS ta tabbatar da cewa an samu karin kudin ne domin inganta fasfon Najeriya da kara masa martaba a fadin duniya.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng