Bidiyo: Dirama yayin da Gwamna Ya Kakare, Ya Gaza Furta Adadin Kasafin Kudi a Majalisa
- Gwamna Monday Okpebholo ya gabatar da kasafin kudin 2025 a gaban Majalisar dokokin jihar Edo ranar Talata, 10 ga watan Disamba
- Wani bidiyo da ake yaɗawa ya nuna gwamnan na kokarin furta jimullar kudin da kasafin zai laƙume kimanin Naira biliyan 605 amma ya kakare
- Duk da abin da ya faru Gwamna Okpebholo ya ci gaba da gabatar da kasafin inda ya ce an ware kashi 37% a ɓangaren harkokin yau da kullum
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Jihar Edo - Wanin abin al'ajabi ya afku a zauren Majalisar dokokin jihar Edo yayin da Gwamna Monday Okpebholo ke gabatar da kasafin kudin 2025 a yau Talata.
A wani bidiyo da ya karaɗe kafafen sada zumunta, an ji gwamnan na ta ƙoƙarin furta jimullar kasafin kudin a gaban ƴan Majalisar dokokin.
Wani ɗan siyasa, Ose Ananih ya wallafa bidiyon a shafinsa na manhajar X wanda aka fi sani da Twitter.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Gwamnan Edo ya gabatar da kasafin 2025
A yau Talata, 10 ga watan Disamba, 2024, Gwamna Okpebholo ya gabatar da kasafin kuɗin 2025 wanda ya kai kimanin Naira biliyan 605 a Majalisar jihar Edo.
Kasafin kuɗin wanda aka yi wa taken, "kasafin sabunta fata na Edo mai tasowa," ya ƙaru da kaso 25 cikin 100 idan aka kwatanta da kasafin 2024.
A cikin jawabinsa, Okpebholo ya bayyana cewa kashi 37 cikin 100 na kasafin kudin; kimanin Naira biliyan 223, an ware su ne ga harkokin yau da kullum.
Ya ce sauran ragowar kuma watau Naira biliyan 381, kashi 63% za su tafi ne ɓangaren manyan ayyuka.
Gwamna ya yi tuntuɓen furta N605bn
Sai dai yayin da yake gabatar da kudirin kasafin kudin, gwamnan ya yi tuntuɓe wajen furta jimullar kuɗin da kasafin zai ci kimanin Naira biliyan 605.
An ji Gwamna Okpebholo yana ƙoƙarin furta jimullar kudin amma yana kakarewa, sai ya dawo farko kuma ya sake kakarewa, ya yi hakan kusan sau uku.
Ma'aikatan Edo za su karɓi albashin watan 13
A wani labarin, an ji cewa Gwamna Monday Okpebholo ya amince a biya ma'aikatan Edo albashi na watan 13 domin ƙara musu ƙwarin gwiwar gudanar da ayyukansu
Monday Okpebhoo ya kuma amince da ɗaukar ɗaliban jihar waɗanda suka kammala digiri da sakamako mafi kyau aiki.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng