Kasafin 2025: Majalisa Ta Yi Barazana, Za a Iya Hana Ma'aikatun Gwamnati Kudin Kashewa
- Majalisar dattawa za ta hana wasu ma'aikatu da hukumomin gwamnatin tarayya kasafin kudin shekarar 2025
- An yi barazanar ga dukkanin hukumomin da suka ki bayyana domin kare kasafin kudin da gwamnati ta ware masu
- Shugaban kwamitin majalisar mai binciken kudi, Sanata Sani Musa ya ce ba za su lamunci kin zuwa kare kasafin ba
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
FCT Abuja - Majalisar dattawa ta yi barazanar ga dukkanin ma’aikatu da hukumomin gwamnati da za su ki bayyana a gabanta domin kare kasafin kudinsu.
Majalisar ta ce hukumomin za su fuskanci babban kalubale a wajen samun kasafinsu na shekarar 2025 matukar ba su halarci zaman kare kansu ba.
Jaridar Vanguard ta wallafa cewa ‘yan majalisar sun ce matakin da za su dauka shi ne haramtawa dukkanin ma’aikatun gwamnati da hukumomin da ba su kare kansu kasafinsu ba.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Majalisa ta bayyana rahoton kudin shiga
Jaridar Punch ta bayyana damuwa game da rashin daidaito a rahoton kudin shiga da yadda aka kashe kudi daga wasu daga cikin ma’aikatun gwamnatin tarayya.
Haka kuma majalisar ta bukaci a kara samun hadin gwiwa tsakaninta da ofishin akanta janar na kasa domin samun ingantattun bayanai a kan batun.
'Yan majalisa sun nemi karin bayanin kashe kudi
Kwamitin majalisar dattawa kan binciken kudi, ya shaida akanta janar ta kasa, Oluwatoyin Madein, cewa ba su ji dadin sabanin alkaluma da aka samu a kan kashe kudin ma’aikatu ba.
Shugaban kwamitin, Sanata Sani Musa ya nemi a magance matsalar domin ta na kawo rauni wajen tafiyar da gwamnati.
An shawarci majalisa kan kudirin haraji
A wani labarin, kun ji cewa tsohon kwamishinan kudi na Kano, Farfesa Kabiru Isa Dandado ya shawarci kwamitin da majalisar dattawa ta kafa da ta lura da wasu bangarori a kudirin haraji.
Farfesa Dandago ya ce akwai bukatar a lura da maganar harajin gado, karin harajin VAT da salon yadda za a tattara da rarraba haraji a tsakanin jihohin da ke fadin kasar.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng