"Ana Jin Jiki:" Kusa a APC Ya Fadi Makomar Tinubu Idan Za a Sake Zabe a Najeriya

"Ana Jin Jiki:" Kusa a APC Ya Fadi Makomar Tinubu Idan Za a Sake Zabe a Najeriya

  • Kusa a jam'iyya mai mulki ta APC ya bayyana cewa tabbas 'yan kasar nan su na cikin mawuyacin hali a yanzu
  • Barista Ismael Ahmed ya ce ko shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu ya tabbatar da cewa 'yan kasa na cikin wahala
  • Jigon ya kara da bayar da tabbacin zai yi wahala shugaban ya sake nasara idan har za a yi zabe a wannan halin

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

FCT AbujaKusa a APC, Barista Ismael Ahmed ya tabbatar da mawuyacin halin da ‘yan Najeriya se ke ciki a wannan gwamnati ta Bola Ahmed Tinubu.

Barista Ahmed ya bayyana cewa zai yi wahala a iya fadi lokacin da ‘yan kasa za su fita da halin yunwa da babu da su ke fuskanta a halin yanzu.

Kara karanta wannan

Zamfara: 'Yan bindiga sun yi fatali da kudin fansa, sun fadi dalilin raina Naira miliyan 3

Tinubu
Jigon APC na ganin Tinubu zai fadi zabe Hoto: Asiwaju Bola Ahmed Tinubu
Asali: Facebook

A wani bidiyo da Abdul-Aziz Na’ibi Abubakar ya wallafa a shafinsa na X, jigon APC ya kara da cewa babu yadda za a iya boye halin matsi da ‘yan kasar nan su ka fada.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ismael Ahmed ya fadi haka ne a wata hira da Seun Okinbaloye ya yi da shi a shirinsa.

Jigon APC ya fadi makomar Tinubu

Barista Ismael Ahmed ya bayyana cewa zai yi matukar wahala shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu ya yi nasara a zabe idan har za a gwabza a yanzu.

Ismael Ahmed ya ce;

“Zai yi wahala, zai zama zabe mai wahala, tabbas. Zai zama zabe mai sarkakiya idan za a yi shi yau.”

Kusa a APC ya kalubalanci gwamnatin Tinubu

Daya daga cikin kusoshin jam’iyya mai mulki ta APC, Barista Ismael Ahmed ya ce akwai bukatar masana tattalin arziki a gwamnati su sanar da ‘yan kasa halin da ake ciki.

Kara karanta wannan

'Ka saɓa da annabi': Malamin Musulunci ya dura kan Sanusi II game da kalamansa

Ya bayyana cewa su kadai ne za su iya fayyace lokacin da mutanen Najeriya za su fara sharbar romon tattalin arzikin da aka ce ana gyawara, saboda haka akwai bukatar su yi bayani.

An kafa kwamitin sulhu a jam'iyyar APC

A wani labarin, kun ji cewa rikicin jam'iyya mai mulki ta APC ya kara kamari a Adamawa, inda aka kafa kwamitin mutum takwas domin warware matsalolin.

Kwamitin, wanda ya gudanar da taronsa a Yola karkashin jagorancin mataimakin shugaban APC na Arewa maso Gabas, Mustapha Salihu, ya fara neman bakin zaren kalubalen.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.