"Ba Mu Son Kowa Ya Kwana da Yunwa," Shugaba Tinubu Ya Shirya Wadata Abinci a Najeriya
- Shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu ya kudiri aniyar wadata ƴan Najeriya da abinci ta yadda babu wanda zai kwanta da yunwa
- Ƙaramin minista noma da samar da abinci, Aliyu Abdullahi ya ce za su yi duk mai yiwuwa wajen ganin abinci ya wadata a ƙasar nan
- Wannan dai na zuwa ne a lokacin da ƴan Najeriya ke ci gaba da nuna damuwa kan hauhawar farashin kayan abinci
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Abuja - Gwamnatin tarayya ta bayyana cewa shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya ɗauki lamarin wadatar da abinci da matuƙar mutummanci.
Ƙaramin ministan noma da tsaron abinci, Aliyu Abdullahi ya ce daga hawa mulki a watan Mayu, 2023 zuwa yanzu, Bola Tinubu ya ɓullo da tsare-tsaren wadata abinci a ƙasar nan.
Ministan ya faɗi haka ne a shirin 'Sunrise Daily' wanda gidan talabijin na Channels ya watsa a ranar Litinin, 9 ga watan Disamba, 2024.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Gwamnatin Tinubu za ta kawo ƙarshen yunwa
A ƴan shekarun nan musamman bayan rantsar da Bola Tinubu, farashin kayan abinci ya yi tashin gwauron zabo a Najeriya.
Masifar tsadar abinci da ake fama da ita a Najeriya na nema ta fi ƙarfin talaka, inda miliyoyin mutane suka wayi gari a cikin yunwa.
Sakamakon haka ne gwamnatin tarayya da sauran gwamnatoci suka ɓullo da wasu shirye-shiryen agazawa talakawa wanda ya ƙunshi rabon kayan abinci.
A bara, ‘yan watanni ƙalilan bayan hawansa mulki, shugaba Tinubu ya ayyana dokar ta-baci kan samar da abinci.
"Burin Tinubu abinci ya wadata" - Minista
Da yake jawabi, karamin ministan noma, Aliyu Abdullahi ya ce:
"Batun wadata abinci ga ƴan ƙasa na cikin abubuwan da muka fi bai wa fifiko a ɓangaren harkokin noma. Bayan haka wadatar abinci zai taka rawa wajen kawar da fatara."
"Shugaba Bola Tinubu ya ɗauki batun samar da abinci da muhimmanci kuma da gaske yake yi, ya damu da halin karancin abinci da ake ciki a ƙasar nan.
Bari na faɗa maku wani abu, sau da yawa shugaban ƙasa ya faɗa mana cewa yana son mu kai Najeriya matsayin da babu wanda zai kwana da yunwa. Za mu cimma hakan."
Gwamnatin Legas ta ɗauko hanyar kawo sauƙi
Kun ji cewa a daidai lokacin da ake fama da tsadar kayan abinci, gwamnatin jihar Legas ta fara shirin cika kasuwanni da shinkafa mai rahusa.
Gwamna Babajide Sanwo-Olu ya ɗauko wannan hanyar ne da nufin sauke farashin kayan abinci ta yadda takalawa za su iya sayen shinkafa.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng