Gwamnan Zamfara Ya yi Sauye Sauye, Ya Nada Sabon Kwamishina

Gwamnan Zamfara Ya yi Sauye Sauye, Ya Nada Sabon Kwamishina

  • Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, ya rantsar da sabon kwamishina da zai wakilci karamar hukumar Kaura Namoda
  • Haka zalika gwamna Lawal yi sauye-sauye kan mukaman wasu kwamishinoni domin inganta ayyukan majalisar zartarwa
  • Gwamnan ya yi kira ga sabon kwamishinan da sauran masu mukamai da su jajirce wajen aiwatar da ayyukan ci gaba a jihar

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Zamfara - Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, ya jagoranci taron majalisar zartarwa inda ya rantsar da sabon kwamishina mai wakiltar karamar hukumar Kaura Namoda.

Hakan ya biyo bayan sauye-sauyen da gwamnan yi yi a cikin majalisar domin tabbatar da ingantaccen aikin gwamnati.

Zamfara
An rantsar da kwaminishina a Zamfara. Hoto: Sulaiman Bala Idris
Asali: Facebook

A sanarwar da mai magana da yawun gwamnan, Sulaiman Bala Idris ya wallafa a Facebook, an bayyana cewa sabon kwamishinan, Kasimu Sani Kaura, ya maye gurbin Mannir Muazu Haidara.

Kara karanta wannan

Abba zai biya kudin makarantar talakawan da Ganduje ya yi biris da su

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Hon. Mannir Muazu Haidara ya yi murabus daga mukaminsa ne bayan zabensa a matsayin shugaban karamar Hukumar Kaura Namoda.

An rantsar da kwamishina a Zamfara

A yayin rantsarwa, Gwamna Lawal ya bayyana cewa an zabi Kasimu Sani Kaura ne saboda nagartarsa da irin gudunmuwar da yake bayarwa ga al’ummarsa da jihar baki daya.

Rahoton Channels Television ya nuna cewa gwamnan ya ce nada Kasimu na nuna irin kudirin gwamnatinsa na amfani da basirar kwararru domin cimma muradun ci gaban jihar.

Dauda Lawal ya yi kira ga sabon kwamishinan da ya sadaukar da kansa wajen hidima ga al’umma tare da yin aiki kafada da kafada da sauran membobin majalisar zartarwa.

Sauye-sauyen da aka yi a majalisar zartarwa

Gwamnan ya bayyana cewa ya yi sauye-sauye na wasu kwamishinoni dominn tabbatar da cewa kowanne mukami yana hannun wanda ya dace.

Sabon kwamishinan ya karbi ragamar Ma’aikatar Muhalli da Albarkatun Kasa, yayin da aka tura Hon. Mahmud Mohammed Abdullahi Ma’aikatar Yada Labarai da Al’adu.

Kara karanta wannan

Za a yi aikin sama da Naira Tiriliyan 4 a masarautar Arewa da ta nada Tinubu Jagaba

Haka zalika, Dr. Nafisa Muhammad ta koma Ma’aikatar Lafiya, inda ta maye gurbin Dr. Aisha M. Anka, wacce aka tura Ma’aikatar Harkokin Mata da Ci gaban Al’umma.

Matasan Zamfara sun tura bukata ga Tinubu

A wani rahoton kun ji cewa kungiyar matasan APC a Zamfara ta nemi shugaba Bola Tinubu ya dawo da Yazid Danfulani shugabancin hukumar SMDF.

Matasan sun bukaci Bola Ahmed Tinubu ya dawo da nadin Danfulani tare da hakura da Hajiya Fatima Umaru-Shinkafi a shugabancin hukumar.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng