Jigon PDP Ya Gano Kuskuren Tinubu kan Kudirin Haraji Na Gwamnatinsa

Jigon PDP Ya Gano Kuskuren Tinubu kan Kudirin Haraji Na Gwamnatinsa

  • Segun Sowunmi ya bayyana kuskuren shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu wajen ƙudirin haraji da gwamnatinsa ta ɓullo da shi
  • Jigon na jam'iyyar PDP ya bayyana cewa Tinubu ne ya jawo adawar da ake yi kan ƙudirin harajin da aka gabatar gaban majalisa
  • Ya bayyana cewa dole ne sauran mutanen wasu ƙabilu su yi ɗar-ɗar da ƙudirin saboda waɗanda suka jagoranci samar da shi duk Yarbawa ne

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

FCT, Abuja - Wani jigo a jam’iyyar PDP, Segun Sowunmi, ya yi magana kan adawar da ake yi kan kuɗirin haraji na gwamnatin Bola Tinubu.

Segun Sowunmi ya ce shugaban ƙasa Bola Tinubu ne ke da alhaki kan adawar da ta biyo bayan ɓullo da ƙudirin harajin da gwamnatinsa ta yi.

Jigon PDP ya caccaki Tinubu
Segun Sowunmi ya soki Tinubu kan kudirin haraji Hoto: Ajuri Ngelale, Segun Sowunmi
Asali: Facebook

Segun Sowunmi, ya bayyana hakan ne yayin wata tattaunawa da tashar Channels tv a ranar Lahadi.

Kara karanta wannan

Zaben 2027: Atiku ya maida martani bayan Akume ya bukaci ya hakura da takara

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Jigon na PDP ya caccaki Tinubu kan naɗa ƴan ƙabilarsa a matsayin ministan kuɗi, shugaban hukumar FIRS, gwamnan babban bankin Najeriya (CBN) da kuma shugaban kwamitin gyaran haraji.

Kuskuren Tinubu wajen ƙudirin haraji

Jigon na PDP ya ce duk da cewa ƙudirin harajin yana da kyau, amma shugaban ya haifar da rashin yarda a tsakanin ƴan Arewa, inda ake zargin ya ƙi sanya mutanen yankin a tawagar tattalin arziƙi da gyaran haraji.

"Su (Tinubu da tawagarsa) ne suka ƙirƙiro matsalar da kansu. Bai yiwuwa a ce shugaban hukumar FIRS, ministan kuɗi, shugaban kwastam da gwamnan CBN duk Yarbawa. Ba a yin hakan."
"Sai kwatsam kawai Yarbawa su fito su ce mun yi sabon tsarin haraji. Su (mutanen sauran ƙabilu) za su ji tsoro."
"Mutane sun je majalisar wakilai ko majalisar dattawa ne domin kare muradun jama’arsu, shi yasa suka je can. Su ne wakilan jama'arsu. Shi ya sa ƙudirin ke fuskantar turjiya."

Kara karanta wannan

'Dan takarar shugaban kasa ya yabi Tinubu ana batun kudirin haraji

- Segun Sowunmi

Ƙudirin harajin Tinubu ya raba ƴan majalisa

A wani labarin kuma, kun ji cewa ƙudirin harajin da gwamnatin shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ta ɓullo da shi ya raba kan ƴan majalisar dattawa.

Wasu daga cikin sanatoci sun fito sun nuna goyon bayansu kan ƙudirin, yayin da wasu kuma suka nuna adawarsu da shi.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng