Ana Batun Kudirin Haraji, Kungiya Ta Fara Yi Wa Sanata a Arewa Barazanar Kiranye
- An fara taso sanata mai wakiltar Bauchi ta Kudu a majalisar dattawa, Shehu Buba Umar, a gaba kan rashin taɓuka abin kirki
- Wata ƙungiyar siyasa ta yi barazanar yi wa sanatan kiranye saboda gaza cika alƙawuran da ya ɗauka lokacin yaƙin neman zaɓe
- Ƙungiyar ta ba shi wa'adin sati ɗaya kan ya gyara siyarsa ko kuma ta ci gaba da shirinta na ganin ya dawo gida daga majalisa
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Jihar Bauchi - Wata ƙungiyar siyasa mai suna Concern Citizens Forum ta yi barazanar yin kiranye ga Sanata mai wakiltar Bauchi ta Kudu, Shehu Buba Umar.
Ƙungiyar ta yi barazanar yi wa Sanata Shehu Buba kiranye ne kan rashin cika alƙawuran da ya ɗauka a lokacin yaƙin neman zaɓensa.

Asali: Facebook
Ƙungiya na shirin yi wa sanata kiranye
Ƙungiyar ta bayyana hakan ne a yayin wani taron manema labarai da ta gudanar a ranar Lahadi, cewar rahoton jaridar Tribune.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ƙungiyar ta gargaɗi sanatan da ya gyara siyasarsa, ya koma kan tsarin da ya yi daidai da alƙawuran da ya ɗauka kafin zaɓe.
Ƙungiyar wacce ta ƙunshi mambobi daga dukkan ƙananan hukumomi bakwai na Bauchi ta Kudu, ta ba sanatan wa’adin sati ɗaya.
An ba sanata wa'adi ya gyara kura-kuransa
Ta ba da wa'adin na sati ɗaya ne ga sanatan, kan ko ya gyara kura-kuransa ko kuma za ta tattaro mambobinta da sauran mutanen mazaɓar, domin ci gaba da shirin yi masa kiranye.
Nasiru Sa’idu Hardo, wanda ya karanta sanarwar bayan taron, ya bayyana cewa:
"Sanata Shehu Buba ya gaza taɓuka komai a zauren majalisa, duk da alƙawuran da ya ɗauka a lokacin yaƙin neman zaɓe."
"Sanata Shehu Buba ya gaza samar da ingantaccen wakilci ga al’ummar Bauchi ta Kudu."
"Bai ƙaddamar da wani aiki mai ma’ana ko wani shiri da zai amfani mutanenmu ba. Muna ba shi dama ta ƙarshe domin ya gyara kura-kuransa, idan ba haka ba za mu ci gaba shirin yi masa kiranye."

Kara karanta wannan
Gwamna da 'yan tawagarsa sun yi batan hanya, sun tsinci kansu a tsakiyar 'yan ta'adda
- Nasiru Sa'idu Hardo
DSS za ta binciki sanata
A wani labarin kuma, kun ji cewa hukumar tsaron farin kaya (DSS), ta fara binciken Sanata mai wakiltar Bauchi ta Kudu a majalisar dattawa, Shehu Buba da alaka da ta'addanci.
Ana zargin Sanata Shehu Buba da alaka da rikakken ɗan ta'adda, sannan tuni aka miƙa.ƙorafin ga shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu.
Asali: Legit.ng