"Mutane ba Su Son Mu": Shugaba Tinubu Ya Fadi Sauyin da Ya Kawo a Najeriya
- Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya bayyana cewa abubuwa da dama sun canza a ƙasar nan tun bayan hawansa mulki
- Tinubu ya bayyana cewa abubuwa za su gyaru a ƙasar nan nan ba da jimawa domin ana kan hanyar da ta dace
- Shugaban ƙasan ya kuma ba da tabbaci ga ƴan Najeriya na tabbatar tsaro da zaman lafiya a ƙasar nan
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
FCT, Abuja - Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya bayyana cewa abubuwa sun fara ɗaukar hanyar gyaruwa, duk da cewa wasu mutanen ba su son gwamnatinsa.
Shugaba Tinubu ya ce duk da ƙalubalen da ake fuskanta a ƙasar nan, gwamnatinsa ta samar da ci gaba, inda ya yi nuni da cewa abubuwa za su gyaru nan gaba.
Me Tinubu ya ce kan tattalin arziƙi?
Tinubu wanda ya samu wakilcin Nuhu Ribadu ya bayyana hakan ne a cibiyar nazarin tsaro ta ƙasa, a birnin Abuja, ranar Asabar, cewar rahoton jaridar Daily Trust.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
"A yau abubuwa na faruwa a ƙasarmu. Ta yiwu mutane ba su sonmu. Suna da abin da ba su yarda da shi ba. Amma abubuwa na canzawa, kuma Najeriya za ta canza."
"Tattalin arziƙi yana canzawa Abu ne mai tsauri, mai matuƙar wahala, muna fuskantar ƙalubale mai girma. Amma ina ba ku tabbaci, ci gaba na nan tafe."
- Shugaba Bola Tinubu
Tinubu zai dura kan masu aikata laifuka
Shugaba Tinubu ya kuma tabbatarwa ƴan Najeriya ƙudirin gwamnatinsa na tabbatar da tsaro da zaman lafiya a ƙasar nan.
Ya ce mutanen da ke aikata laifuka, za su fuskanci shari'a ba tare da la'akari da inda suke zaune ba, rahoton tashar Channels tv ya tabbatar.
"Idan kai mugun mutum ne, ko kana cikin Najeriya ko a waje kana cikin matsala. Za mu bi ka. Za mu tabbatar ka fuskanci hukunci."
- Shugaba Bola Tinubu
Tinubu ya kori shugaban hukuma
A wani labarin kuma, kun ji cewa shugaban ƙasa Bola Tinubu ya maye gurbin wasu mutane huɗu da ya naɗa muƙamai a hukumar raya yankin Kudu maso Gabas (SEDC).
Mai girma Bola Tinubu ya maye gurbin Emeka Atuma inda ya naɗa Emeka Nworgu a matsayin sabon shugaban hukumar SEDC.
Asali: Legit.ng