Tsohon Gwamna Ya Fadi Hukuncin da Ya Dace da Masu Kashe Jami'an Tsaro
- Tsohon gwamnan jihar Neja ya nuna takaici kan yadda ake samun masu kashe jami'an tsaro a Najeriya
- Mu'azu Babangida Aliyu ya bayyana cewa hukuncin kisa shi ne abin da ya dace da masu kashe jami'an tsaro
- Tsohon gwamnan ya nuna cewa yin hakan zai ƙarfafa gwiwar jami'an tsaro masu aikin kare rayuka da dukiyoyin al'umma
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
FCT, Abuja - Tsohon gwamnan jihar Neja, Mu’azu Babangida Aliyu, ya bayyana hukuncin da ya dace da masu kashe jami'an tsaro.
Mu'azu Babangida Aliyu ya bayyana cewa duk duk wani mutum ko gungun mutanen da suka kashe wani jami’in tsaro, abin da ya dace da su shi ne kisa.

Source: Facebook
Tsohon gwamnan na Neja ya bayyana haka ne a cibiyar nazarin tsaro ta ƙasa (NISS) da ke Abuja, cewar rahoton jaridar Leadership.

Kara karanta wannan
Tsohon gwamna a Arewa ya saba da 'yan yankin, ya soki masu caccakar kudirin haraji
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
'Kisa ya dace da masu kashe jami'an tsaro', Muazu Aliyu
Mu'azu Babangida ya ce ɗaukar irin wannan matakin zai ƙarfafa gwiwar jami’an tsaro, rahoton Vanguard ya tabbatar.
Tsohon gwamnan ya ƙara da cewa domin kare jami’an tsaro dole ne Najeriya ta samar da wani tsari wanda ya tanadi hukuncin kisa ga duk wanda ya kashe jami’an tsaro.
Muazu Babangida ya yi mamakin dalilin da zai sanya wani ya kashe jami'an tsaro yayin da suke bakin aiki kuma a bar shi ya tafi haka nan.
"Na yi farin ciki hafsan hafsoshin tsaro, Janar Christopher Musa yana wajen nan. Ko da yake, sun ce CDS ko sojoji ba su da hannu a wajen samar da tsare-tsare."
"Amma bari na faɗi haka, ban ga wata ƙasa da za a kashe kusan sojoji 38 ba kuma a yi shiru. Ina so na ba da shawarar cewa duk wanda ya kashe jami'in tsaro dole ne ya mutu!"
- Mu'azu Babangida Aliyu
Ƴan bindiga sun farmaki ƴan banga
A wani labarin kuma, kun ji cewa wasu ƴan bindiga sun kashe ƴan banga bakwai a ƙaramar hukumar Mariga ta jihar Neja.
Ƴan bindigan sun kashe ƴan bangan ne waɗanda ke raka manoma kai amfanin gona a Makogi/Ungwan Elbi da ke ƙaramar hukumar Mariga ta jihar Neja.
Asali: Legit.ng
