Sauki Ya Zo: Farashin Kayan Abinci Ya Yi Kasa a Kasuwa

Sauki Ya Zo: Farashin Kayan Abinci Ya Yi Kasa a Kasuwa

  • Sauƙi ya zo a birnin Akure na jihar Ondo yayin da farashin kayayyakin abinci ya yi ƙasa sosai a kasuwa
  • Buhun ya zaftare N20,000 daga farashin da ake sayar da shi a baya na N55,000 inda ya koma N35,000 yanzu
  • Taliya, shinkafa da wake duk sun yi ƙasa, yayin da farashin manja da tattasai suka yi tashin gwauron zabi

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Ondo - Farashin wasu kayayyakin abinci ya ragu matuƙa a Akure, babban birnin jihar Ondo. 

Farashin kayayyakin abincin ya yi ƙasa sosai yayin da ake ci gaba da kokawa kan tsadar rayuwa a Najeriya.

Farashin kayan abinci ya sauka a Ondo
Farashin kayayyakin abinci ya sauka a birnin Akure na jihar Ondo Hoto: Mohammed Owais Khan
Asali: Getty Images

Jaridar The Nation ta rahoto cewa farashin buhun kwaki ya ragu daga N55,000 zuwa N35,000, yayin da kwandon tumatur ya ragu daga N80,000 zuwa N60,000. 

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Farashin kayan abinci ya sauka a Ondo

Farashin buhun shinkafa mai nauyin kilogiram 50 ya ɗan yi ƙasa kaɗan daga N93,000 zuwa N90,000.

Kara karanta wannan

Shugaba Tinubu ya kaɗu da rasuwar babban malamin addinin Musulunci a Najeriya

Haka kuma, kwalin taliya wanda a da ake sayar da shi a kan Naira 35,000 ya koma N23,000.

Bugu da kari, farashin buhun wake mai nauyin kilogiram 50 ya yayo ƙasa daga N250,000 zuwa N130,000.

Manja ta ƙara tsada

Sai dai, farashin manja da tattasai ya yi tashin gwauron zabi. 

Farashin jarkar manja mai cin lita 25 ya tashi daga N37,000 zuwa N54,000, sannan tattasai ya tashi daga N15,000 zuwa N45,000. 

Karanta wasu labaran kan farashin kayan abinci

Jigon APC ya koka kan tsadar abinci

A wani labarin kuma, kun ji cewa wani jigon jam'iyyar APC a jihar Osun, Mista Olatunbosun Oyintiloye, ya ce tsadar kayan abinci ya fara zama bala'i a halin da ake ciki a ƙasar nan.

Ya koka kan cewa galibin magidanta ba su samun abinci mai kyau, wasu ma sai sun fita sun yi bara ko sun roƙa sannan za su ci.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng