Tsohon Gwamna a Arewa Ya Saba da 'Yan Yankin, Ya Soki Masu Caccakar Kudirin Haraji

Tsohon Gwamna a Arewa Ya Saba da 'Yan Yankin, Ya Soki Masu Caccakar Kudirin Haraji

  • Tsohon gwamnan jihar Niger, Mu'azu Babangida Aliyu ya barranta da yan Arewa kan sabon kudirin haraji a Najeriya
  • Babangida Aliyu ya koka kan yadda mutane ke korafi game da harajin inda ya ce mafi yawansu ba su fahimci komai a ciki ba
  • Hakan ya biyo bayan kawo sabon kudirin haraji da wasu ke ganin zai yi rugu-rugu da tattalin arzikin Arewacin Najeriya

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

FCT, Abuja - Tsohon gwamnan jihar Niger, Babangida Aliyu ya yi magana kan kudirin haraji da ake ta ce-ce-ku-ce.

Tsohon gwamnan ya caccaki masu adawa da kudirin gyaran haraji inda ya bukaci sake duba kan tsarin.

Tsohon gwamna ya soki masu sukar dokar kudirin haraji
Tsohon Gwamnan Niger, Mu'azu Babangida Aliyu ya goyi bayan kudirin haraji. Hoto: Mu'azu Babangida Aliyu.
Asali: Facebook

Kudirin haraji: Tsohon gwamna ya soki yan Arewa

Babangida Aliyu ya bayyana haka ne a yau Asabar 7 ga watan Disambar 2024 a Abuja yayin wani taro, cewar Tribune.

Kara karanta wannan

'Majalisa ta fi karfin a yi mata barazana': Akpabio ya ja kunne kan kudirin haraji

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A cewarsa, masu adawa da kudirin mafi yawansu ba su dauki lokaci don nazari mai zurfi kan dokar ba.

Aliyu ya kuma soki gwamnati kan gazawarta wajen isar da sako game da wannan kudirin haraji domin wayar da kan jama'a.

Tsohon gwamnan ya kara da cewa ya zama wajibi ‘yan kasa su fahimci cewa babu wata doka ko tsari da zai amfanar da kowa iri daya.

Mu'azu Babangida ya shawarci al'umma kan kudirin

"Na tattauna da Nuhu Ribadu lokacin da muke cikin dakin taro na ce masa duba kaga, da yawa daga cikin wadanda suke muhawara kan wannan kudiri na haraji ba su karanta shi ba."
"Amma kuma akwai matsalar isar da sako, ya zama dole gwamnati ta rika magana a fili musamman idan galibin jama’a ba su da ilimi sosai."
"Ya kamata ku zama na farko wajen bayyana kowanne tsari musamman wanda zai kawo sauye-sauye domin jama’a su fahimce shi."

Kara karanta wannan

Kudirin Haraji: Gwamnatin Tinubu za ta rika karbar haraji a kudin gado?

- Mu'azu Babangida Aliyu

Sultan ya ba da shawara kan kudirin haraji

Kun ji cewa Majalisar Koli ta Harkokin Addinin Musulunci (NSCIA) ta yi kira ga al'umma da su kwantar da hankulansu kan kudirin haraji.

Majalisar karkashin shugabancin Sarkin Musulmi, Sa'ad Abubakar ta ce sun yi ganawa kan kudirion kuma sun fahimci inda aka dosa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.