Ana Jimamin Tashin Bama Bamai a Zamfara, Wani Abu Ya Sake Fashewa a Najeriya
- Wani sinadari da aka ajiye a cikin kwalabe ya tarwatse, ya haddasa tashin wuta a yankin Agege da ke jihar Legas
- Rahoanni sun bayyana cewa wata mata ta tsalle rijiya da baya yayin da jami'an kashe gobara suka kai ɗauki wurin a kan lokaci
- Daraktar hukumar kashe wuta ta Legas, Misis Margaret Adeseye ta ce sun fara gudanar da bincike domin gano wanda ya ajiye sinadarin a tsakar rana
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Lagos - Wata mata da har yanzu ba a tantance sunanta ba, ta tsallake rijiya da baya sakamakon fashewar wani sinadari wanda ya yi sanadin tashin gobara a Legas.
Lamarin ya faru ne a gida mai lamba 291 a gefen tsohon titin Abeokuta daura da makarantar sakandiren Vetland da ke yankin Agege.
Wani abu ya tarwatse a jihar Legas
Vanguard ta ruwaito cewa jami'an hukumar kashe gobara da wasu masu ba da agajin gaggawa ne suka yi hanzarin ceto matar lokacin da suka kai ɗauki wurin.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Rahotanni sun bayyana cewa lamarin ya faru ne da misalin karfe 6 na yammacin ranar Juma’a, 6 ga watan Disamba.
Jami'an hukumar kashe gobara na Agege sun yi nasarar shawo kan wutar da ta tashi sakamakon fashewar wasu kwalabe ɗauke da sinadarin da ba a tantance ba har yanzu.
Kwalaben da ke ɗauke na sinadarin na ajiye ne a wani fili da aka kewaye shi da katanga a anguwar.
Wane mataki mahukunta suka ɗauka?
Daraktar hukumar kashe gobara ta Legas, Misis Margaret Adeseye, ta ce binciken farko da aka gudanar ya nuna gobarar ta tashi ne bayan fashewar sinadarin.
Adeseye ta ce yanzu haka hukumar ta fara bincike don gano mamallakin kayan da kuma kalar sinadarin da ya ajiye a tsakar rana domin ɗaukar matakin da ya dace.
"Matar da aka ceto na kwance a asibiti ana mata maganin raunin da ta samu," in ji Adeseye.
Gobara ta laƙume kadarori masu tsada
A wani labarin, kun ji cewa gobara ta laƙume dukiyoyi na miliyoyin Naira a sabuwar kasuwar zamani da ke Lafia, babban birnin jihar Nasarawa.
Musa Abdullahi, ɗaya daga cikin waɗanda shagunansu suka ƙone a kasuwar ya ce babu wanda ya san musabbabin tashin wutar.
Asali: Legit.ng