Tinubu Ya Kori Shugaban Hukuma Kasa da Awa 24 bayan Ba Shi Mukami
- Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya yi sauye-sauye a hukumar raya yankin Kudu maso Gabas na Najeriya (SEDC)
- Tinubu ya maye gurbin mutumin da ya naɗa a matsayin shugaban hukumar ƙasa da sa'o'i 24 bayan ya ba shi muƙamin
- Naɗe-naɗen da shugaban ƙasa mai girma Bola Tinubu, ya yi dai na buƙatar amincewar majalisar dattawan Najeriya
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
FCT, Abuja - Shugaban ƙasa Bola Tinubu ya maye gurbin wasu mutane huɗu da ya naɗa muƙamai a hukumar raya yankin Kudu maso Gabas (SEDC).
Shugaba Tinubu ya naɗa Emeka Nworgu a matsayin sabon shugaban hukumar inda ya maye gurbin Emeka Atuma.
Bayo Onanuga, mai ba shugaban ƙasa shawara na musamman kan harkokin yada labarai da dabaru, ya bayyana hakan a shafinsa na X ranar Asabar.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Tinubu ya yi sauye-sauye a hukumar SEDC
Onanuga ya ce Tinubu ya kuma maye gurbin dukkanin manyan daraktoci uku da aka naɗa da farko tare da naɗa ƙarin daraktoci guda biyu.
Sauyin ya zo ne ƙasa da sa'o'i 24 bayan Tinubu ya miƙa jerin sunayen waɗanda aka naɗa a hukumomin SEDC da NWDC ga majalisar dattawa domin tantancewa.
Onanuga ya ce Tinubu ya cire Donatus Nwankpa a matsayin daya daga cikin ƴan majalisar hukumar SEDC.
"Sabon babban daraktan kuɗi shine Stanley Ohajuruka, wanda ya maye gurbin Anthony Ugbo. Toby Okechukwu shine sabon babban daraktan ayyuka, ya maye gurbin Obinna Obiekweihe."
"Cif Sylvester Okonkwo ya maye gurbin Dr Daniel Ikechukwu Ugwuja. Manyan daraktocin biyu da aka naɗa ba tare da muƙami ba sune Chidi Echeazu da Dr Clifford Ogbede."
- Bayo Onanuga
Tinubu ya soke naɗin shugaban hukuma
A wani labarin kuma, kun ji cewa shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu ya sauya shawara game ɗa naɗin shugaban asusun kula da harkokin haƙar ma'adanai watau SMDF/PAGMI.
Shugaba Tinubu ya soke naɗin Yazid Shehu Danfulani a matsayin wanda zai shugabanci SMDF/PAGMI, ya ce babu wurin da za a naɗa wani a hukumar.
Asali: Legit.ng