Badaru Ya Fadi Dalilin Tinubu Na Bashi Ministan Tsaro a Gwamnatinsa
- Ministan tsaron Najeriya, Mohammed Badaru, ga taɓo batun muƙamin da ya samu a gwamnatin Shugaba Bola Tinubu
- Mohammed Badaru ya bayyana cewa rawar da ya taka a lokacin da yake mulkin jihar Jigawa, ta taimaka masa wajen samun muƙamin minista
- Ministan ya bayyana cewa hanyoyin da ya bi wajen samar da tsaro a Jigawa na taimaka masa a yanzu da yake kan ministan tsaron Najeriya
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
FCT, Abuja - Ministan tsaro, Mohammed Badaru, ya yi magana kan samun muƙamin da ya yi a gwamnatin Shugaba Bola Tinubu.
Mohammed Badaru ya bayyana cewa an ba shi muƙamin ministan tsaro ne saboda ƙwarewarsa a wajen gudanar da mulki.

Asali: Facebook
Ministan ya bayyana hakan ne yayin wata tattaunawa da jaridar Daily Trust.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Naɗin da aka yi wa Badaru a matsayin ministan tsaro, ya sa an kauce daga al'adar naɗa mutanen da ke da alaƙa da harkar tsaro a muƙamin.
Badaru ya magantu kan zama ministan tsaro
Sai dai, Badaru ya bayyana cewa rawar da ya taka a lokacin da yake gwamnan Jigawa, ta taimaka wajen samun muƙamin ministan da ya yi.
"Naɗin da Shugaba Tinubu ya yi min na ministan tsaron Najeriya, ya nuna kaucewa daga al'adar naɗa mutanen da ke da tarihin aikin soja."
"An yi shi ne bisa gogewar da na samu a fannin gudanar da mulki, da kuma nasarorin da aka samu a fannin magance rikice-rikice, musamman a matsayina na tsohon gwamnan jihar Jigawa."
"Hanyar da na bi wajen samar da tsaro a Jigawa ya haifar da haɗin kai tsakanin masu ruwa da tsaki. Ƙwarewar da na samu ta yi tasiri a matsayina na ministan tsaro."
- Mohammed Badaru
Badaru ya yi ta'aziyyar rasuwar Lagbaja
A wani labarin kuma, kun ji cewa ministan tsaron Najeriya, Mohammed Badaru Abubakar ya yi magana kan rasuwar Laftanar-janar Taoreed Lagbaja.
Mohammed Badaru ya jajantawa shugaban ƙasa Bola Tinubu kan rasuwar hafsan sojoji da aka yi a Najeriya inda ya ce mutuwsrsa babban rashi ne.
Asali: Legit.ng