'Yan Kasuwa Sun Tafka Asara, Wuta Ta Babbake Miliyoyin Naira a Nasarawa
- Gobara ta laƙume dukiyoyi na miliyoyin Naira a sabuwar kasuwar zamani da ke Lafia, babban birnin jihar Nasarawa
- Musa Abdullahi, ɗaya daga cikin waɗanda shagunansu suka ƙone a kasuwar ya ce babu wanda ya san musabbabin tashin wutar
- Hukumar kashe gobara ta jihar Nasarawa ta tabbatar da aukuwar lamarin, ta ce an tura jami'an kwana-kwana tun da wuri
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Jihar Nasarawa - Wata gobara da ta afku ta kone shagunan ɗinki da dama a sabuwar kasuwar zamani da ke Lafiya, babban birnin jihar Nasarawa.
Bayanai sun nuna cewa mummunar gobarar ta lalata kayayyaki masu ɗumbin yawa da suka kai darajar miliyoyin Naira.
Gobara ta tafka ɓarna a Nasarawa
Wakilin jaridar Daily Trust da ya ziyarci wurin da lamarin ya faru ya gano cewa gobarar ta tashi ne a daren Alhamis da misalin karfe 9:30 har zuwa washe garin Juma'a.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ma’aikatan hukumar kashe gobara ta jihar Nasarawa sun gamu da tsaiko a ƙoƙarinsu na kashe gobarar saboda tarin tarkace a ciki da wajen kasuwar.
Haka nan kuma zafin wutar mai raɗafi ya yi ta mayar da ƴan kwana-kwana baya, lamarin da ya kawo cikas a kokarin da suke yi na ganin sun shawo kan gobarar.
Shaguna 30 sun ƙona a ibtila'in gobara
Da yake labarta abin da ya faru, Musa Abdullahi, wanda shagonsa na cikin wadanda suka kone, ya ce babu wanda zai iya tantance musabbabin tashin gobarar.
Ya bayyana cewa akalla shaguna 30 ne suka ƙone a gobarar, inda ya ce kashi 70 cikin 100 na shagunan da lamarin ya shafa na dinki ne da ke dauke da sababbin kekuna.
Musa Abdullahi ya ce:
“An kawo sababbin injinan dinki arba’in da safiyar Alhamis, kuma duk sun lalace a gobarar, tare da shaguna uku mallakar mahaifina.
Hukumar kashe gobara ta tabbatar da lamarin
Daraktan hukumar kashe gobara ta jihar Nasarawa, magini Ombogus-Joshua, ya tabbatar da faruwar lamarin, kamar yadda The Cable ta kawo.
Ya ce sun samu kiran gaggawa da misalin karfe 9:30 na daren Alhamis kuma nan take aka tura jami’an kashe gobara zuwa wurin.
Wuta ta laƙume kaya a ma'ajiyar NSIPA
A wani labarin, mun kawo maku cewa gobara ta yi ɓarna a wurin adana kaya na hukumar NSIPA mai kula da shirye-shiryen walwala da zamantakewar ƴan Najeriya.
An ahoto cewa cewa gobarar ta lakume kayan horar da matasa masu cin gajiyar shirin N-Power a daidai lokacin da suke jiran a biya su kudinsu.
Asali: Legit.ng