Ana Zancen Kudirin Haraji, An Sa Rana da Lokutan Shirya Zanga Zanga
- Omoyele Sowore ya sanar da shirya zanga-zanga a Najeriya da kasashen waje domin neman sakin Dele Farotimi
- An ruwaito cewa lauya Dele Farotimi ya gurfana a kotun majistare ta Ado-Ekiti bayan zarge-zargen da ya musanta
- Lamarin zanga zangar na zuwa ne yayin da ake tsaka da zancen kudirin haraji da shugaba Bola Tinubu ya tura majalisa
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
FCT, Abuja - 'Dan takarar shugaban kasa a 2023, Omoyele Sowore ya sanar da shirya zanga-zangar lumana a wasu jihohi.
Za a gudanar da zanga zangar ne domin neman sakin lauyan mai kare haƙƙin ɗan Adam, Dele Farotimi, wanda ke tsare a gidan gyaran hali na Ekiti.
A cewar sanarwar da Yele Sowore ya wallafa a shafinsa na Facebook, zanga-zangar za ta gudana a Abuja, Legas, Ado-Ekiti, da ma birnin London.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Dele Farotimi: Dalilin shirya zanga zanga
Sowore ya bayyana cewa manufar zanga-zangar ita ce nuna rashin amincewa da tsare lauyan tare da kiran hukumomin Najeriya su mutunta haƙƙin bil’adama.
Zanga-zangar za ta fara da karfe 7 na safe a agogon Najeriya a ranar Litinin, 10 ga Disamba, inda mutane za su taru a wuraren kamar:
- Ma’aikatar shari’a da babbar kotun tarayya, Abuja.
- Hedikwatar ‘yan sanda ta Ado-Ekiti.
- Ofishin Afe Babalola, Legas.
- King’s College London.
Kama Dele Farotimi ya jawo zanga-zanga
Arise News ya wallafa cewa Farotimi ya shiga hannu ranar Talata, bayan jami’an ‘yan sanda daga Ekiti sun tsare shi a Legas ba tare da sanar da rundunar ‘yan sanda ta jihar ba.
Rahotanni sun ce an kama shi ne bisa zargin rashin amsa gayyata da ‘yan sanda suka yi masa a Ekiti, wanda hakan ya sa aka tasa keyarsa zuwa jihar domin gurfanar da shi a kotu.
Kotun Ekiti ta umarci a tsare Farotimi
Kotun majistare ta Ado-Ekiti ta ba da umarnin a tsare Farotimi a gidan gyaran hali har zuwa ranar 10 ga Disamba, lokacin da za a cigaba da sauraron karar.
A yayin zaman kotun ranar Laraba, Farotimi ya musanta dukkan zarge-zargen da suka haɗa da tuhumar ɓata suna da rashin biyayya ga doka, kamar yadda mai gabatar da kara ya bayyana.
Kotu ta yanke hukuncin kisa a Jigawa
A wani rahoton, kun ji cewa wata kotu a jihar Jigawa ta yanke hukuncin kisa ta hanyar rataya kan mutane hudu bisa zargin yin sihiri da kuma kisan kai.
Wadanda aka kama sun hada da miji da mata da wasu danginta, wadanda aka same su da laifin kashe Salamatu Musa a 2019.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng