Yadda Sanusi II Ya yi Zaman Fada duk da Jigbe Jami'an Tsaro a Gidan Sarkin Kano
- Sarkin Kano, mai martaba Muhammadu Sanusi II ya gudanar da zama a cikin fadar Kofar Kudu duk da jibge jami’an tsaro
- Har yanzu ba a samu bayani daga rundunar ‘yan sandan Kano kan dalilin jibge jami’an tsaron a kofar Kudu ta masarautar ba
- Gwamna Abba Kabir Yusuf na wata tafiya a kasar Indiya, yayin da al’amuran masarautar ke kara jan hankalin jama’ar Najeriya
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II ya bayyana cikin kayan sarauta na gargajiya a ranar Juma’a domin gudanar da zaman fada a Kofar Kudu.
Mai martaba Muhammadu Sanusi II ya yi zaman fadan ne duk da jibge jami’an tsaro da aka yi a wajen masarautar.
Jaridar Leadership ta wallafa cewa sarkin ya ci gaba da gudanar da harkokinsa cikin nutsuwa tare da wasu hadiman fadar.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Menene dalilin kewaye masarautar Kano?
Har zuwa yanzu, rundunar ‘yan sandan jihar Kano ba ta bayar da wani karin bayani kan jibge jami’an tsaro a fadar ba.
A yanzu haka dai lamarin ya haifar da ce-ce-ku-ce kan abin da ke wakana tsakanin masarautar da 'yan sanda.
Haka zalika, masarautar ba ta fitar da wata sanarwa kan ko sarkin zai ci gaba da shirin tafiyar sa zuwa garin Bichi domin halartar wani taro da aka tsara ba.
Me Abba Kabir ya ce kan lamarin?
Rahotanni daga gidan gwamnati sun nuna cewa gwamna Abba Kabir Yusuf yana wata tafiya zuwa kasar Indiya domin wani aiki.
Wasu na ganin rashin gwamnan a kusa alama ce ta babu wata kwakkwarar hanyar warware matsalar a cikin gaggawa.
Masana na ganin lamarin zai iya yin tasiri mai girma a cikin al’amuran siyasa da al’adu na jihar Kano.
Gwamnati Kano ta yi magana kan mamaye fada
A wani rahoton, kun ji cewa gwamnatin Kano ta ce abin mamaki ne yadda ƴan sanda suka kewaye fadar mai martaba Sarkin Kano, Sanusi II.
Sakataren gwamnatin jihar, Abdullahi Baffa ya ce sarki ya tsaya raka Wanban Kano zuwa yankinsa a garin Bichi amma 'yan sanda suka hana.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng