"Ka da Ku Zauna a Duhu," Gwamna Ya Buƙaci Ƴan Najeriya Su Karanta Kudirin Haraji

"Ka da Ku Zauna a Duhu," Gwamna Ya Buƙaci Ƴan Najeriya Su Karanta Kudirin Haraji

  • Gwamnan Imo ya yi kira ga ƴan Najeriya su ware lokaci su karanta baki ɗaya abin da ke kunshe a kudirin harajin Bola Tinubu
  • Hope Uzodinma ya ce bai dace mutane su tsaya suna sukar kudirin a cikin duhu ba tare da sanin alherin ko akasin haka da ya ƙunsa ba
  • Gwamnan ya bayyana cewa a ganinsa kudirin yana da amfani domin wani tsari ne da zai kawo ƙarin kuɗin shiga ga gwamnati

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Imo - Gwamna Hope Uzodimma na jihar Imo ya yi kira da a yi taka-tsan-tsan game da kudirin saura fasalin haraji na shugaban ƙasa, Bola Tinubu.

Uzodinma, shugaban ƙungiyar gwamnonin APC ya roƙi ƴan Najeriya su tsaya su karanta duk abin da kudirin ya ƙunsa kuma su fahimta kafin yanke hukunci.

Kara karanta wannan

Gwamnonin Najeriya sun yi Allah wadai da tashin bam a jihar Zamfara

Gwamna Hope Uzodinma.
Gwamnan Imo ya bukaci ƴan Najeriya su zauna su fahimci abin da ke kunshe a kudirin haraji Hoto: Hope Uzodinma
Asali: Facebook

Gwamna Uzodinma ya magantu kan kudirin haraji

Gwamnan ya yi wannan furucin ne a gidan gwamnatinsa da ke Owerri, babban birnin jihar Imo jiya Alhamis, kamar yadda Channels tv ta ruwaito.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Mika kudirin da shugaba Bola Tinubu ya yi ga majalisar dokokin kasar ya haifar da zazzafar muhawara a tsakanin ‘yan Najeriya.

Gwamnonin Arewa, sarakuna da Malaman addininin Musulunci na cikin waɗanda suka yi fatali da sabon tsarin harajin.

Da yake martani, Gwamna Uzodimma ya ce wasu daga cikin wadanda ke adawa da kudirin harajin ba su san ainihin abin da ya ƙunsa ba.

Gwamnan Imo ya ba ƴan Najeriya shawara

"Mafi akasarin mu da ke sukar waɗannan kudirorin ba mu zauna mun nazarci abubuwan da suka ƙunsa ba balle mu fahimci amfani da rashin amfanin tsarin ba.
"Saboda haka ina kira gare mu baki ɗaya, mu samu lokaci mu karanta kudirorin dokar nan ta haraji, mu gano wuraren da aka yi kuskuren don yin sukar da hujja.

Kara karanta wannan

Gwamnan Legas ya yi magana kan kudirin harajin Tinubu, ya maida martani ga Zulum

"Baya ga haka, ni ina ganin cewa wani kudiri ne na tattalin arziki wanda ake son ƙara tarawa gwamnati kudi da daidaita tsarin haraji, sannan kuma zai kawo ma kasar nan wani nau’i na tsantseni."

- Hope Uzodinma.

Gwamnan Legas ya goyi bayan kudirin haraji

A wani labarin, kun ji cewa Gwamna Babajide Sanwo-Olu na jihar Legas ya ce galibin masu ɓaɓatu kan kudirin haraji ba su san me ya ƙunsa ba.

Gwamnan ya kuma musanta ikirarin da wasu ƴan Arewa suka yi cewa jihar Legas ce za ta amfani da kudiirn, yana mai cewa ba gaskiya ba ne.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262