An Kama Rikakken 'Dan Boko Haram da Ya Fara Barazana a Kudancin Najeriya
- Hukumar NSCDC reshen Ekiti ta cafke wani da ake zargin ɗan Boko Haram ne mai suna Isiah Jafaru, wanda aka fi sani da "Nabida," a garin Iloro
- Rahotanni sun nuna cewa wanda ake zargin ya tsere daga yankin Arewa maso Gabas bayan farmakin da sojoji ke kaiwa kan Boko Haram
- Hukumar NSCDC ta tabbatar da cewa za ta ba wa DSS wanda ake zargin don ci gaba da bincike mai zurfi da kuma yin hukuncin da ya dace
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Ekiti - Hukumar NSCDC reshen Jihar Ekiti ta samu nasarar kama wani mutum da ake zargi da zama babban ɗan kungiyar Boko Haram, Isiah Jafaru wanda aka fi sani da Nabida.
An kama wanda ake zargin ne a Iloro Ekiti, bayan jami'an NSCDC sun fara bincike kan halayensa masu ban tsoro da suka bayyana.
Jaridar Daily Trust ta wallafa cewa mai magana da yawun hukumar NSCDC, SC Afolabi Tolulope ya tabbatar da kama Nabida.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
SC Afolabi Tolulope ya ce binciken farko ya nuna cewa Nabida babban mamba ne a kungiyar Boko Haram, wanda ya koma garin Iloro Ekiti bayan ya tsere daga Arewa maso Gabas.
Jami'an NSCDC sun sa kafar wando da Boko Haram
Kwamandan NSCDC na jihar Ekiti, Dr. Sosina Paul ya bayyana cewa hukumar ta kafa ƙungiyar bincike da yaki da ta'addanci domin hana mayakan Boko Haram sake taruwa.
Dr. Sosina Paul ya tabbatar da cewa hukumar za ta yi aiki tare da sauran hukumomin tsaro domin tabbatar da cewa an ci gaba da samun zaman lafiya a jihar.
Hukumar NSCDC ta yi kira ga jama'an Ekiti
The Cable ta wallafa cewa shugaban NSCDC ya yi kira ga jama'ar Ekiti da su kasance masu lura da kuma sanin maƙwabtansu.
Ya ja hankalin sarakunan gargajiya da su rika dubawa da kyau game da wadanda ke amfani da filayensu, musamman kango.
Ya kuma shawarci jama’a da su gaggauta kai rahoto idan suka ga mutum ko gungun mutane da ke nuna halaye na daban ga ofishin jami'an tsaro mafi kusa.
Sojoji sun saki wuta kan Boko Haram
A wani rahoton, kun ji cewa rundunar sojin saman Najeriya ta yi nasarar hallaka mayakan kungiyar Boko Haram jihar Borno.
Rahotanni sun tabbatar da cewa sojojin Najeriya sun saki bom kan Boko Haram ne yayin da suke tsaka da wata tattaunawa domin kulla makirci.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng